Jima’i ya zama wasan motsa jiki, za a yi gasar fidda gwaninsa a Sweden
Karuwanci da kafa gidan karuwai a kasar haramun ne bisa dokar kasar.
A wani abu mai kamar almara kasar Sweden ta mayar da jima’i wasan motsa jiki a hukumance.
Ma’ana mu’amalar da aka sani tsakanin jinsi don samar da zuri’a da kuma biyan bukata, a kasar ta koma tamkar wasan kwallo ko kokawa ko kuma wasan langa, a cewar rahotanni.
- SEC ta haramta hadar-hadar ‘Binance’ a Najeriya
- Folashodun Adebisi: Wane ne Gwamnan CBN na rikon kwarya?
Sannan ana nan ana shirye-shiryen gudanar da gasar jima’i ta farko a karshen makon nan domin fid-da- gwani na gwanaye a karon farko a nahiyar Turai.
Masu takara a wannan sabon wasan da aka kira motsa jiki kafin su zama zakaru, ana bukatar su yi jima’i a kowace rana har na tsawon awa shida.
A cewar rahotannin jaridun kasar, wasu alkalai ne za su fitar da zakarun gasar jima’in, haka ma ’yan kallo za su taka rawa wajen wannan zabe ta hanyar sharhi da bayyana ra’ayoyi da kuma nazarin zaben da alkalan suka yi.
An shirya gasar fid-dagwanin jima’in ne, inda masu gogayya da juna ko kuma ’yan wasa za su kara da juna ta hanyar yin jima’i a kullum na tsawon minti 45 zuwa awa daya.
Rahoton ya kuma ce, mataki uku ne a gasar kuma kafin mutum ya kai ga mataki na gaba, sai ya samu wani adadi na maki a kowane mataki tukunna.
Masu yin takara a gasar ta jima’i za su iya samun maki 5 zuwa 10 a kowane mataki, amma wannan maki ba zai tabbata ba sai an hada da na ’yan kallo da kuma na alkalai biyar da ke sa- ido a kan gasar.
Haka kuma, rahoton ya kuma ce za a rika yin gasar jima’in ne a bainar jama’a, wadanda za su lura da yanayin yin jima’in don yin alkalanci.
Wasu abubuwan da za a yi la’akari da su wajen bayar da makin sun hada da daidaito masu jima’i, kwarewarsu na iya jima’i, juriyarsu da kuma sauran muhimman abubuwa duk za su zama cikin lissafin wanda zai zama zakara.
Shugaban Kungiyar Wasan Motsa Jiki na jima’i, Mista Dragan Bratych ya ce, yana fatan wata rana jima’i zai zama daya daga cikin wasannin motsa jikin da za rika yi a duk duniya.
Ya kafa hujja da muhimmancin jima’i ga ilimi da kuma inganta lafiyar jiki da na kwakwalwa da mu’amillar take sa wa dan adam.
Ya ce, “kamar kowane wasan motsa jiki, ba za ka samu wani sakamako mai kyau ba in babu atisaye.”
Ya kuma bayyana cewa, wani babban abin a-zo-a-gani game da wanna nau’in wasan motsa jiki shi ne sa wa abokin karawarka farin ciki, domin ba kamar sauran wasannin motsa jiki ba, inda a ke gudun yada kanin wani.
A nan zakara a jima’i shi ne wanda ya iya gamsar da abokin karawarsa, ba kamar a sauran wasannin motsa jiki ba, da faduwa a kodayaushe ke kai wa ga bakin cikin da takaici.
Sai dai wani abin mamaki game da wannan kasa shi ne duk da wannan gasa, karuwanci da kafa gidan karuwai a kasar haramun ne bisa dokar kasar.
Sai dai wasu rahotanni na cewa wannan ikirarin da kuma shirya gasar yunkuri ne na wani mutum wanda ya tura takardar neman izinin, kuma yake jiran amincewar hukumar kula da wasanni ta kasar.