Jin tsoron Allah na hakika (1)
Godiya ta tabbata ga Allah Mai daukaka wanda ya yi maSa da’a, Mai kaskantar da wanda ya saba maSa, Ya girmama wanda Ya so ta hanyar bin umurninSa da yin nesa daga abin da Ya hane shi. Ina gode maSa Mai tsarki da daukaka, ina yi maSa shukura bisa abin da Ya yi mana na […]
Godiya ta tabbata ga Allah Mai daukaka wanda ya yi maSa da’a, Mai kaskantar da wanda ya saba maSa, Ya girmama wanda Ya so ta hanyar bin umurninSa da yin nesa daga abin da Ya hane shi. Ina gode maSa Mai tsarki da daukaka, ina yi maSa shukura bisa abin da Ya yi mana na ni’ima.
Na shida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Shi ke da buwaya da girma. Na shaida Shugabanmu Annabi Muhammad bawan Allah ne, zababbe a tsakanin daukacin talikai, shugaban masu da’a. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa masu girma da da’a.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku tuna tsayuwarku a gaba gare Shi, “A ranar da kowane rai zai je yana jayayyar tunkudewa daga kansa, kuma a cika wa kowane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba.” (k: 16:111). Ya ku Musulmi! Idan akwai wani cikin mutane da yake ruduwa da rayuwar duniya da kama kasa da ya yi, kuma yake bin son zuciyarsa tare da jahiltar ingantacciyar akida, kuma ya koma yana tsoron duk abin da yake jin hadari ne da ke yi masa barazana, ko sharri da zai mamaye shi, ko wata katanga da za ta hana shi isa ga burinsa da samun nasarar bukatunsa, to, ya sani a cikin bayin Allah akwai wanda yake bin hanya totar, yana tafiya a kan tafarki madaidaici, yana mai gudun hanyar ma’abuta rudu da kai-kawo, mai kauce wa hanyar ma’abuta shakku da raunin imani! Su suna bin hanyar Allah, bi na wanda ya san Ubangijinsa ya koma gare shi, ba sa tsoron kowa koma bayanSa, ba su kwadayin komai sai daga gare Shi, su ne wadanda suka san matsayin tsoron Allah a matsayin wani babban matsayi da ake saukar da masu bautar Allah a ciki, masu neman taimako daga gare Shi, kuma shi ne mafi amfani ga zuciya, kuma mafi girman abin da yake tasiri a rayuwa a nan duniya da Lahira.
Ku sani tsoro farilla ne a kan kowane dan Adam kamar yadda Allah Ya nuna cikin fadinSa: “Wancan Shaidan ne kawai yake tsoratar da ku, masoyansa. To kada ku ji tsoronsu, ku ji tsoroNa, idan kun kasance masu imani.” (k: 3: 175). Da kuma: “To kada ku ji tsoron mutane, kuma ku ji tsoroNa.” (k:5:44).
Kamar yadda Allah Madaukaki Ya yi kyakkyawar yabo ga ma’abuta tsoronSa cikin fadinSa: “Lallai ne wadanda suke masu sauna saboda tsoron Ubangijinsu. Da wadanda suke game da ayoyin Ubangijinsu suna imani. Da wadanda suke game da Ubangijinsu ba su yin shirki. Da wadanda ke bayar da abin da suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace domin suna komawa ga Ubangijinsu. Wadancan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri, alhali kuwa suna masu tserewa zuwa gare su (ayyukan alheri).” (k:23:57-61).
Kamar yadda Alhasan (Allah Ya yi masa rahama) ya fada, wannan ya faru ne, saboda sun yi ayyukan da’a sun yi kokari a cikin haka, sun ji tsoron kada a mayar musu a ki karba musu, domin shi mumini yana hada aikin kwarai ne da tsoro, yayin da munafuki yake hada munantawa da amincewa, wato amince wa ukuba.
Kuma Allah Madaukaki Ya yabi wasu daga cikin Mala’ikunSa Makusanta da suka siffantu da wannan siffa, sai Ya ce, “Suna tsoron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umurninsu.” (k: 16:50). Sannan Ya yabi AnnabawanSa (AS), bisa siffantuwa da tsoronSa: “Kuma wadanda suke iyar da Manzancin Allah, kuma suna tsoronSa, kuma ba su tsoron kowa face Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi.” (k:33:39).
Yayin da tsoron Allah ya zamo damfare da ilimi, to, gwargwadon sani da ilimi, gwargwadon tsoron Allah ga mutum, don haka ne Manzon Allah (SAW) ya fi daukacin halittu tsoron Allah, kamar yadda ya bayyana a Hadisin da Buhari ya fitar a cikin Sahihinsa inda yake cewa: “Na rantse da Allah, ni ne na fi su (duk halitta), sanin Allah, kuma na fi su jin tsoronSa.” A lafazin Muslim kuma “Wallahi ina zaton kasancewa na fi ku tsoron Allah, kuma mafi sanin abin da ke sa a ji tsoronSa.” Kuma ya sake cewa: “Da kun san abin da na sani da kun yi dariya kadan, kuma kun yi kuka da yawa, kuma da ba ku ji dadi da mata a shimfidu ba, kuma da kun fito kuna kuka zuwa ga Allah.” Imam Ahmad ya fitar da shi a Musnad dinsa, sannan Tirmizi a Jami’insa da isnadi mai kyau.
Za mu cigaba insha Allah