Jinjina ga matar Gwamnan Jihar Kebbi

A yau idan akwai wata matar gwamna a duk fadin yankin Arewa ko ma daukacin fadin kasar nan da za a iya bai wa kambun yabawa, godiya da  jinjinar ban girma,to ba za ta wuce Dokta Zainab Atiku  Bagudu (matar gwamnan jihar Kebbi) ba. Wannan mata  jaruma ce, hazika ce hadima ce, domin ko ba […]

Jinjina ga matar Gwamnan Jihar Kebbi

A yau idan akwai wata matar gwamna a duk fadin yankin Arewa ko ma daukacin fadin kasar nan da za a iya bai wa kambun yabawa, godiya da  jinjinar ban girma,to ba za ta wuce Dokta Zainab Atiku  Bagudu (matar gwamnan jihar Kebbi) ba. Wannan mata  jaruma ce, hazika ce hadima ce, domin ko ba komai ta taimakawa mijinta, ta  kuma taya shi fita kunyar talakawansa.

Koda yake Barewa ba ta yi gudu danta ya yi rairafe ba, domin Zainab Bagudu ’ya ce ga Alhaji Ummaru Aliyu Shinkafi (Marafan Sakkwato), wanda kowa ya san shi babban Jarumi ne a ma’aikatar ‘yan sandan ciki,wanda ya rike mukamin babban darakta a ma’aikatar tsaro ta Najeriya. Mahaifiyarta kuwa babbar lauya ce da ta amsa kiran mukamin lauya tun cikin shekaru fiye da talatin da suka gabata.

Bayan kammala karatun sakandare  a Kwalejin  Sarauniya (kueens Collage)  da ke Legas a cikin  shekarar 1984, Zainab Shinkafi ta yi nasarar yin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,a inda ta yi digirinta na farko a fannin likitanci. Bayan nan kuma ta tafi  Ingila domin yin karatun kwarewa a fannin likitan yara, daga bisani kuma ta sake yin digiri na biyu a fannin likitan yara. Ta kuma kara yin difiloma a Royal College da ke Ingila don kara samun horo na musamman a kan lafiyar Yara da kuma zamowa daya daga cikin mambobin kungiyar likitocin yara na duniya.

Bayan dawowarta gida Najeriya a shekara ta 2002, Hajiya Zainab Bagudu ta riki mukamin babbar jami’a mai kula da sashen kananan Yara na asibitin Garki da ke babban birnin tarayya Abuja. A shekara ta 2009 ne Likita Zainab ta fara shirinta na tsere sa’anni, domin ta kirkiro wata Cibiya da ake kira ‘Medicaid Cancer Foundation.’  Medicaid cibiya ce da aka ginata ta musamman don duba lafiyar al’umma tare da taimakon nagargartun na’urori, domin an wadata ta da na’urorin binciken cututtuka iri daban-daban, kuma wadanda suke tafiya tare da zamani (na’urorin). Akwai irin su MRI (na’urar hoton sassan jiki na ciki),CT scan (na’urar akwatin da ake saka mutum don ganin hoton dukkanin cutukan da ke jikinsa), Endoscopy (na’urar gano cutukan da ke cikin Hanji da tace su),Echocardiology (na’urar auna bugun zuciya da matsayin lafiyarta) da dai sauransu  da ba mu anbata ba. Har wa yau cibiya ce da ake duba lafiyar kananan yara mai zaman kanta.

Hajiya Zainab, zamowarta matar babban gwarzon dan kishin kasa,watau Alhaji Abubakar Atiku Bagudu,tun yana Sanata har zamowarsa gwamnan Jihar Kebbi, ya ba ta dama, ya kara mata azama da zammar ganin ta kusantu ga talakawa kamar yadda ta dade tana cin burin ganin ta yi hakan, watau  bada gagarumar gudunmawa ga ingata lafiyar rayuwar talaka, musamman mata, kananan yara, da kuma tallafawa matasa a hanyoyin cigaban rayuwarsu.

Gaskiya Hajiya Zainab Allah yana sonta,kuma Yana girmamata,domin duk wanda  ya ci burin yin wani abun  alfanu ga al’ummarsa, kuma burinsa ya cika tiryan-tiryan ba tare da matsaloli ko wasu shahararrun kalubale da suka hana shi cikarsa ba,to, lalle Allah Yana son sa da alheri, Ya zabe shi, kuma Yana girmama shi, wannan kuwa shi ne matakin da Hajiya Zainab Bagudu take a kai a yau, domin dukkanin tunaninta yana kan lafiyar talaka da ci gabansa ne kawai. 

 Abin da ya sa muka anbata hakan kuwa shi ne,idan ka yi duba da irin tarin tulin ayukan ci gaban al’ummar kasar nan da take aiwatarwa musamman ga jama’ar jihar Kebbi da kuma na jahar haihuwarta watau Jihar Sakkwato abin sai wanda ya ji ya gani. 

Mu dauki misali da wannan shekara ta 2017 kadai mu gani, tun daga farkonta (watau Janairu) har zuwa wannan wata na Disanba (karshen shekara), ba a samu wani wata da Dokta Zainab Bagudu ta tsaya don ta huta daga yi wa jama’a hidima ba,aikin kenan kaddamar da ayukan ci gaban al’ummar jihar Kebbi da jihar Sakkwato da Binnin Tarayya Abuja ko kuma dai wata jiha har shekarar ta kare. Bari mu zayyano wasu ayukan  da ta kaddamar a wannan shekarar kawai, domin ku shaida kuma ku kara gaskata fadar da muka yi na cewa Zainab Bagudu ce  Jarumar Matan Gwamnonin kasar nan, ga ayukan a jere kamar haka:- 

Dokta Zainab Bagudu ita ce matar gwamna ta farko a kasar nan da ta kaddamar da yekuwa a kan fahimtar gane cutar daji (cancer) a duk fadin kasar nan. A cikin shekarar nan ce ta kaddamar da cibiyarta ta Medicaid a garin Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi. Ta kaddamar da bada horo na musamman ga ma’aikatan lafiya a Jihar Kebbi a kan sanin yadda ake gane mata masu dauke da cutar dajin nono da ta mahaifa. An tace mata fiye da dubu biyu masu dauke da cutar ,kuma an tallafa masu da bas u magani,ko yi masu aikin fida ga wadanda yanayin jikinsu ya bukaci hakan. Ta kirkiri kungiyoyin yekuwar gane cutar daji a daukacin makarantun gaba da firamare a fadin jihar Kebbi. 

Hajiya Zainab ta kai ziyara a gidan yarin Jihar Kebbi,a inda ta ’yanta mutane talatin da suka kasa biyan tara, ko suka cancanci a yafe masu laifukansu, kuma ta bada kayayyakin more rayuwa ga sauran da aka bari a gidan.

Har wa yau matar gwamnan Jihar Kebbi ta karfafa zukatan matan jihar da su koma gona, a inda ta fara wannan aikin nata da kananan hukumomi hudu na jihar. Ta kai masu taki da iraruwa,ta ba su kudin fara aiki, ta kuma hadasu da malaman gona mashawarta.

Matar gwamnan mace ce mai tausayi domin ko a cikin watan uku na wannan shekarar, tana tafiya ta ci karo da wata mata marar hankali (mahaukaciya) tare da ’yarta Siddika,nan da nan tausayinta ya kamata ta sa aka dauki matar zuwa asibiti, yarinya Siddika kuwa ta nufi gidanta da ita, aka sanyata a makaranta ana kiran yarinyar da suna Siddika Bagudu.

Zainab mace ce mai kula da hidimar addini, domin a kowace shekara cikin watan Azumi sai ta shirya taron wa’azi, don ilmantar da al’umma tare da kara dankon zumunci da tallafawa juna a tsakanin ’yan jihar.

A gaskiya ayukan Hajiya Zainab Bagudu ba sa kirlguwa a wannan shafin, mun dai zakulo kadan daga cikinsu ne kawai don mu nunawa jama’a dalilinmu da ya sa muka kirata da jarumar matan gwamnonin kasar nan.

Hajiya Zainab kin cancanta, kin dace, kuma dole ne jama’ar jiharki da al’ummar kasar nan su yaba miki, kuma su gode miki. Mun gode Allah Ya kara girma da  daukaka amin.

A’isha Usman Liman 09093467171