Jinjina ga Shugaba Buhari da sojojin Najeriya kan dawo da ’yan matan Dapchi

Assalamu alaikum, bayan gaisuwa da fatan alheri.  A yau ina so in yi sharhi ne da yabo game da jajircewar da Rundunar Sojin Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wajen dawo da ’yan matan Sakandaren Kimiyya da ke garin Dapchi ta Jihar Yobe. Hakikanin gaskiya a bangaren tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari bai […]

Jinjina ga Shugaba Buhari da sojojin Najeriya kan dawo da ’yan matan Dapchi
Jinjina ga Shugaba Buhari da sojojin Najeriya kan dawo da ’yan matan Dapchi

Assalamu alaikum, bayan gaisuwa da fatan alheri.  A yau ina so in yi sharhi ne da yabo game da jajircewar da Rundunar Sojin Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wajen dawo da ’yan matan Sakandaren Kimiyya da ke garin Dapchi ta Jihar Yobe.

Hakikanin gaskiya a bangaren tsaro, Shugaba Muhammadu Buhari bai yi kasa a gwiwa  ba idan muka yi la’akari da yadda aka sace ’yan matan Chibok a baya.  Wasa-wasa yau fiye da shekara hudu ke nan amma har yanzu ba a sako da damansu ba.

A gaskiya yanzu ana samu koma-baya a karatun yara musamman ’yan mata a yankin Arewa maso Gabas, inda iyaye ke fargabar tura ’ya’yansu makaranta don ba su san abin da zai faru ba.  Hakan kuwa ba karamar koma-baya ke janyo wa yankinmu na Arewa da kasar nan baki daya ba.

Idan ba so ake yi ’ya’yanmu su daina yin karatun boko kwata-kwata ba, to ya kamata gwamnati ta tashe tsaye wajen kawo karshen kai hare-haren da ’yan Boko Haram suke yi musamman a makarantun kwanan dalibai da ke yankin Arewa maso Gabas.

A bangare daya,  zan ba gwamnati da hukumomin tsaro shawarar a rika koyawa ’yan makaranta dabarun gudu da neman mafaka a yayin da suka ji ko suka ga wani abu da ba su yarda da shi a makarantu ko gidajensu ba.

A hakikanin gaskiya hakan zai taimaka wajen kubutar yara ’yan makaranta daga hannun ’yan ta’adda da ke sace su saboda wani dalili na kashin kansu.

Sannan ina ba hukumomin tsaro shawarar su yi kwakkwaran bincike game da yadda aka sace ’yan matan Dapchi da yadda aka janye jami’an tsaro kafin a kai harin. Domin akwai ayar tambaya game da yadda ’yan ta’addan suka je makarantar suka sace daliban, inda suka dauki lokaci mai tsawo suna cin karensu ba babbaka ba tare da jami’an tsaro sun kai dauki ba.

Sannan bayan sun mayar da yaran rahotanni sun nuna har tayar motarsu suka canja da ta yi faci ba tare da an kama wani ko wadansu daga cikin ’yan Boko Haram din ba.  Wai shin ina jami’an tsaron suke ne?  Ana nufin a ce tun bayan da aka sace yaran har aka koma da su garin Dapchi babu wani matakin tsaro da aka dauka a garin na Dapchi har suka mayar da yaran ba a yi musu komai ba? Ko ko an janye jami’an tsaon ne saboda wata manufa kamar yadda wadansu ke zargi an shirya ne?

Wadannan da ma wasu, su ne amsoshin da ni da kuma dimbin jama’a suke bukatar amsarsu kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya (Amnesty Intertional) ta yi irin wadannan tambayoyi.

A karshe, ina rokon Allahu Subhanahul Wata’ala Ya tabbatar mana da tsaro mai dorewa a kasarmu Najeriya da Afirka da ma duniya baki daya, amin

Nura Sani Rijau (Human Rights Actibist & Public Adbiser) matashi mai rajin kare hakkin dan Adam   08108291641

08026664213