Jinjina ga ‘yan Najeriya kan zaben da suka yi cikin lumana
Nura Sani Rijau Assalamu alaikum Editan jaridar Aminiya mai tarin albarka. Ina so ku ba ni dama in yi yabo da jinjina ga ’yan uwana ’yan Najeriya bisa zaben da suka fito kwansu da kwarkwata suka yi cikin ruwan sanyi da lumana. Babu shakka yanzu kan ’yan Najeriya ya fara wayewa, lura da yadda zaben […]
Nura Sani Rijau
Assalamu alaikum Editan jaridar Aminiya mai tarin albarka. Ina so ku ba ni dama in yi yabo da jinjina ga ’yan uwana ’yan Najeriya bisa zaben da suka fito kwansu da kwarkwata suka yi cikin ruwan sanyi da lumana.
Babu shakka yanzu kan ’yan Najeriya ya fara wayewa, lura da yadda zaben bana ya bambanta da na shekarun da suka shude, inda za ku ga matasa kai har ma da kananan yara wadansu ’yan siyasa marasa kishin kasa na sayen kayan maye da gusar da hankali suna ba su, sannan su sayi makamai su raba musu a lokacin zabe don su je su tayar da hankali. Wani lokaci su tayar da kayar baya a inda ba a yi musu yadda suke so ba su sara ko su kashe wanda suka so. To alhamdulillahi wannan zaben Allah Subhanahu Wata’ala Ya kawar mana da wannan muguwar dabi’a musamman jihohin da aka zaci faruwarsa sai ga shi Allah Ya kare!
A mafi yawan jihohin Najeriya, musamman Arewa ban ji inda aka ce an yi rikici ko tayar da hankali wurin zabe ba, wannan abin alfahari ne da jin dadi ga duk mai kishin kasarmu Najeriya,
Da haka ne kuma nake amfani da wannan dama wajen kara kira ga ’yan kasa musamman matasa da yara cewa a zaben gwamnoni da na na majalisun jihohi da za a yi a mako mai zuwa su natsu su fito kwansu da kwarkwata su yi zabe cikin lumana da kwanciyar hankali, ba hayaniya ba fada kamar yadda suka yi a na Shugaban Kasa da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai.
Ya kamata fa mu lura da wani abu, wadannan ’yan siyasar da ke bai wa matasa kwayoyi da makamai suna bangar siyasa wallahi tallahi ba sa bari ’ya’yansu su fito a yi da su. Ku yi dubi ku gani mana, kun taba ganin dan siyasa a shiyyarku da ’ya’yansa suka fito banga, bayan sun sha kwayoyin maye? Da haka ne za ku gane cewa duk wani dan siyasa ’ya’yansa na birni suna hutawa, idan lokacin saka su makaranta ya yi za su dauke su saka su a manyan makarantu masu tsada su yi karatu, Idan sun kammala karatun kuma za ku ga sun dauke su sun kai su manyan ofisoshin gwamnati suna aiki, mu ko ’ya’yan talakawa muna nan kawai kara zube muna biye da su, shin ba za mu yi hankali ba ?
A karshe ina rokon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya zaba mana shugabanni nagari kuma nagartattu masu kishin kasa da al’ummomin da suke shugabanta ba masu kishin aljifansu ba amin.
Daga Nura Sani Rijau
08108291641/ 08026664213.