Jinjina ta kamaci Janar Buratai da dakarunsa ba jafa’i ba
Ga duk mai bibiyar al’amuran da ke faruwa a Najeriya dangane da harkar tsaro, musamman ma yaki da ‘’yan Boko Haram, ya san cewa a watanni shida da suka gabata, an samu gagarumar nasara. Sai dai da yake al’amarin rayuwa mai wahala ne, an samu wasu da ke kushe da ma jefa wa Hafsan Hafsoshin […]
Ga duk mai bibiyar al’amuran da ke faruwa a Najeriya dangane da harkar tsaro, musamman ma yaki da ‘’yan Boko Haram, ya san cewa a watanni shida da suka gabata, an samu gagarumar nasara. Sai dai da yake al’amarin rayuwa mai wahala ne, an samu wasu da ke kushe da ma jefa wa Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai kalmomin jafa’i da batanci. Shi kuwa mai sharhi kan al’amuran yau da kullum AUWAL G. dANBORNO (08064595353) ya ce jinjina da yabo da addu’ar kirki kawai suka kamace shi. Ga yadda ya warware jigon tsokacinsa:
Duk wanda na ga yana zagin Janar Buratai, nakan dauke shi wanda ba ya kaunar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dubi bawan Allah, hatta bikin Sallah da kowane ma’aikaci ke yi cikin iyalansa, shi tasa Sallar a filin daga ya yi.
Ranar Lahadin da ta gabata, a garin Konduga tare da sojojin Bataliya ta 103 suka sha ruwa a cikin “trench” (irin ramin da sojoji ke hakawa a filin daga yayin yaki). Ba na jin a tarihin rayuwata na taba ganin wani babban soja da ya taba yin haka. Duk da wannan sadaukarwa da nuna jarumta da kwazo, ake samun wasu wawaye suna zagin sa, wasu na bin sa da sharrin wai sai an zubar da kima da darajarsa a idon duniya.
Ya zama dole duk mai hankali da hange, mai son zaman lafiya da ci gaba ya sanya Janar Buratai a cikin addu’ar kariya daga sharrin makiya Arewa, makiya Najeriya da makiya zaman lafiya.
Janar Buratai da sojojin Najeriya sun sadaukar da rayuwarsu domin samun lafiyarmu, mun manta cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne manyan abin da ake bukata, wadanda ke yalwata arziki da walwalar cin arzikin hankali kwance.
Ga duk wanda ya dubi Janar Buratai, zai lura da damuwar matsalar rashin tsaro da son wanzar da zaman lafiya a zuciyarsa da gangar jikinsa suke. Ina da tabbacin cewa Shugaban kasa bai yi zaben tumun dare ba, ya zabo mutum jarumi managarci, wanda ya san matsalar tsaro da maganinta. Kodayake wannan wata al’ada ce, duk wani mai laifi ba ya kaunar ganin wanda ke kokarin tabbatar da hana wanzuwar ’yan Boko Haram ba za su yi farin ciki da shi ba. Masu fasa bututu ba za su so ganin sa ba, masu kokarin kafa gwamnati cikin gwamnati ba za su yi murna da kasancewar sa a doron kasa ba. Kai duk wani mai laifi karami ko babba, ba ya farin ciki da samuwar jarumin mutum irin Janar Buratai.
Ga duk wanda ya san Janar Tukur Buratai, ya san mutum ne mai son zaman lafiya da kokari wajen ganin an tabbatar da gaskiya da jajircewar ganin ba a danne wa kowa hakkinsa ba. Dubi dai yadda ya yi buda baki da kananan sojoji a cikin rami, kawai domin ya karfafa wa kananan sojoji gwiwa da sanya ido wajen ganin sun bayar da himma wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ga duk wanda ke da lissafi, ya juya da tunaninsa baya, ya lissafa irin dubunnan rayukan da ake yin hasara kullum a yankin Arewa, idan mutum na da hankali da lissafi zai kalli Janar Buratai a wani jarumin wannan karni. Dalilin wannan batu bai wuce duk wanda ke yin yaki da miyagu yana yin wata sadaukarwa ne domin wata al’umma ta rayu cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Babu wani yaki da miyagun masu laifi da wai manufarsa shi ne a rasa rayuka ko a yi shahadar da ake kira ‘Shahadar kuda.’ Ya dace al’ummarmu su fahimci cewa tsageranci da rashin kunya ga manya da sarakuna ko shuwagabanni ba wani abin burgewa da tinkaho ko jarumta ba ne. Babu wata jarumta da sadaukarwa da ta wuce kokarin tabbatar da gaskiya da kuma kwato hakkin wanda aka danne wa hakki. Ta ya zan fahimci mutumin da ke tara matasa da zuga su da wanke masu kwakwawa a matsayin mutumin da ke son kawo gyara da ci gaba a cikin al’umma? Ba na zaton zan dauki wani mutum ko malami da ke sanya matasa bijire wa gwamnati ko sarakuna a matsayin wanda ke son ci gaban wadannan matasa. Babu wata al’umma da za ta zama nagartacciya da zagi ko cin fuskar shuwagabanni.
Ba za mu taba mantawa da yanayi na firgici da muka shiga ba a shekarun baya a kasar nan. Ya kasance duk wanda ya sanya kafa ya fita daga gida bai da tabbacin zai dawo cikin iyalansa, ba tare da wani mummunan al’amari ya faru ba. A cikin motar haya fargaba, fargaba a cikin kasuwa, masallatan Juma’a da na khamsu salawat da coci-coci ba a bar su ba. Kasuwanni da tasoshin mota da asibitoci ba su tsira ba, hatta wanda ke tafe a hanya bai tsira ba. Ba mu manta ba cewa mun shiga yanayin da hatta bakon ido tsoron sa ake ji, kowa bai yarda da kowa ba. Kasuwanni da majalisan al’umma sun zama kangwaye, kasuwanci da zirga-zirga sun tsaya cak babu wani abu da ke motsi. Jami’an tsaro na cikin firgici da tashin hankali, wadanda ake tsarewar suna cikin rudu da firgicin rashin tabbacin abin da zai faru safe da yamma ko tsakar dare. Ilimi ya durkushe, domin hatta makarantun kananan yara ba a bar su ba. Duk lokacin da uba ya tura da ko ’yarsa makaranta, babu tabbacin dawowa. Babu aminci tsakanin malamai da daliban ilimi. Malamai da dama tun daga matakin firamare har zuwa jami’a da dama sun rasa rayukansu, haka dalibai tun daga matakin firamare zuwa jami’a sun rasa rayukansu.
Ina zaton har zuwa yanzu ba mu manta yadda duk lokacin da muka fito domin zuwa unguwar da ba ta fi tafiyar minti goma ba zuwa da dawowa, za mu iya share awa biyar ba tare da mun je wajen da muke bukata ba saboda tsabar bincike domin neman tabbatar da tsaro. Garuruwa da dama musamman daga yankin Arewa maso gabas, an hakura da su daga dukkan wata zirga-zirga ta kasuwanci ko makamancin hakan. Garuruwa da dama sun tarwatse, dubunnan iyaye sun rasa ’ya’yansu, haka mata dubunnai sun zama zawarawa. An sha samun jariri na kuka a gefen gawar mahaifiyarsa, an samu kananan yara na yawo a dokar daji ba tare da sanin wajen da za su dosa ba. Yunwa ta kashe mutane dubunnai.
kokari da jajircewar Janar Buratai ta sanya duk wadannan masifu suka zama tarihi walwala da arziki da jin dadi ya fara dawowa a yankin Arewa maso gabas da sauran jihohin Najeriya. A shekaru shida yau a jihohin yankin Arewa maso gabas an samu gabatar da Sallar Idi a masallatai. Idan ba mu manta ba, shekaru shida baya ba a gabatar da bukukuwan Sallah a jihohin, hatta shige da fice ana haramta su ga al’umma, a dalilan rashin tsaro.
Bai kamata mu manta da Janar Buratai a dukkan addu’armu ba, ya dace mu fito mu yaba wa jami’an tsaron Najeriya, mu karfafa masu gwiwa bisa irin wannan kokari nasu. Kowane dan Adam yana bukatar a yaba masa domin kara masa kaimi bisa ayyukan alheri, balle wadanda suka sayar da rayukansu domin tabbatuwar zaman lafiya a tsakanin al’ummar wannan kasa. Muna jinjina da yabawa da goyon baya bisa wannan jajirtaccen gwarzo, bisa sadaukarwa da sallama rayuwarsa domin al’umma. Muna addu’ar Allah Ya tsare gabansa da bayansa, Allah Ya sanya albarka a rayuwarsa da ta zuri’arsa. Allah Ya kiyaye shi a duk wajen da ya samu kansa. Yadda ya fara aikin lafiya, Allah Ya sa ya gama cikin aminci. Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Allah Ya kiyaye, ya kare dukkan fitunu.
***