Jinjiri ya rayu bayan ya kwana 10 a kabari

A ranar Litinin din makon jiya ne ’yan sanda a lardin Guangdi da ke kudancin kasar China suka ceto wani jinjiri bayan an binne shi a cikin wani kabari, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta bayyana. An ruwaito cewa jinjirin an binne shi ne a wani kabari da ke wata makabarta har sai […]

Jinjiri ya rayu bayan ya kwana 10 a kabari
Jinjiri ya rayu bayan ya kwana 10 a kabari

A ranar Litinin din makon jiya ne ’yan sanda a lardin Guangdi da ke kudancin kasar China suka ceto wani jinjiri bayan an binne shi a cikin wani kabari, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta bayyana.

An ruwaito cewa jinjirin an binne shi ne a wani kabari da ke wata makabarta har sai da ya yi kwana 10 kafin ya samu kubuta daga ciki.
An yi amannar dai cewa iyayensa ne suka aika danyen aikin. Kuma sun yi hakan ne saboda wata lalura da aka haife shi da ita, inda lebensa yake a cinye. Kodayake, a kowace shekara ana samun dubban jirajiran da ake yadawa saboda irin wannan lalurar.
An dai haifi wannan jinjirin ne a ranar 20 ga watan jiya. Kuma sai bayan kwana hudu ne aka sallame su daga asibiti saboda zazzabin mai zabi da yake fama da shi, kamar yadda hukumar asibitin ta bayyana.
An ruwaito cewa kwana biyar bayan sallamarsu ne, iyayen jinjirin ciki har da kakarsa suka dauki hayar wani mutum da aka biya shi ladan Dala 290 (kusan naira dubu 60) domin ya batar da yaron.
Kwana 10 bayan hakan, sai wata mata mai tsince-tsincen a shara ta ji kukan jinjiri daga wurin da aka binne shi. Da taimakon wasu mutane aka kira ’yan sanda, wadanda suka tone ramin da yake ciki. Daga nan kuma sai suka garzaya da shi asibiti.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa