Jinkirin nunar doya ne ya kawo tsadarta ba fitar da ita waje ba – Shugaban ’Yan doyar Dawanau

’Yan kasuwar Doya da ke Dawanau a Jihar Kano sun nemi gwamnati a dukkanin matakai da ta taimaka musu, ta hanyar tallafa musu da jarin da za su rika hada-hadar fitar da doya kasashen waje, don bunkasar kasuwancinsu a cewar Shugaban ’yan kasuwar Doya da ke Dawanau a Jihar Kano, Alhaji Ado Mohammed a lokacin […]

Jinkirin nunar doya ne ya kawo tsadarta ba fitar da ita waje ba – Shugaban ’Yan doyar Dawanau

’Yan kasuwar Doya da ke Dawanau a Jihar Kano sun nemi gwamnati a dukkanin matakai da ta taimaka musu, ta hanyar tallafa musu da jarin da za su rika hada-hadar fitar da doya kasashen waje, don bunkasar kasuwancinsu a cewar Shugaban ’yan kasuwar Doya da ke Dawanau a Jihar Kano, Alhaji Ado Mohammed a lokacin da yake tataunawa da Aminiya.

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ta kaddamar da shiri na musamman don fara fitar da doya kasashen waje. Shugaban ya bayyana shirin da gwamnatin tarayyar na fitar da doya kasar waje a matsayin abin da zai kawo ci gaba a kasar. “Wannan shiri na fitar da doya kasar waje ci gaba ne a wurinmu ba wai ci baya kamar yadda jama’a ke tunani ba. Doyar da ake nomawa a kasar nan ta yi mana yawa kwarai da gaske, don haka idan har za a fita da ita za a samu alheri a kasar. Kin ga ita doya ba ta taba yankewa, yanzu wacce aka noma din nan a bana ba za ta kare ba sai ta badi ta zo. Don haka a Najeriya muna da isasshiyar doyar da za mu ci, har mu fita da ita kasar waje. Don haka muna maraba da wannan shiri” Sai dai  Shugaban ya yi korafin cewa ba  su iya shiga tsarin ba, har sai gwamnati ta tallafa musu da jari ko da kuwa bashi ne. 

“Tunda muke ba mu taba samun tallafi daga gwamnati ba ko da kuwa na bashi ne. An sha yi mana alkawurra iri-iri sai dai ba su kai ga cika ba har yanzu, “ inji shi.

Fama-faman da muka cika kuwa ba za su lissafu ba. Kin ga idan ba mu yi shi wannan shirin na fitar da doya kasar waje ba, muna ji muna ganin yana nema ya fi karfinmu, saboda ba mu da jarin da za mu yi harkar cinikayyar kasashen waje. 

Ta yaya mutum mai jarin Naira miliyan daya ko kasa da haka zai iya yin wannan harka. Idan mutum ya ce bankunan kasuwanci zai je ya nemo bashi, to saboda kudin ruwa da zai rika biya za a wayi gari kasuwancinsa ya shiga wani hali na lalacewa. Gwamanti ce kawai take iya bayar da bashi ba tare da karbar kudin ruwa ba.  

A cewarsa: “Don haka muna amfani da wannan kafa wajen yin kira ga gwamnati ta tallafa mana da jarin yin wanann harkar, kuma kananan ‘yan kasuwarmu ma suna bukatar jarin da za su rika gudanar da harkokinsu a cikin kasuwa.”

A yanzu haka muna da mutane sama da 500 da ke cin kasuwa a wannan kasuwa tamu, kama daga kan masu gadi da masu daukar kaya da masu kirgawa da masu zubawa a mota da sauransu. ” 

Alhaji Ado Mohammed ya kuma bayyana jinkirin da aka samu wajen nunar doya da girbe ta a matsayin abin da ya jawo tsadarta ba wai saboda an fara fitar da doyar kasar waje ba. 

“Abin da ke faruwa shi ne yawanci doyar da muke samu a kasuwa ana noma ta ne a jihohin Binuwe da Nassarawa da Filato da Kogi da Neja da Taraba, to sai ya zamanto a wannan lokaci doyar Jihar Kogi ce kawai ta zo kasuwa. Sauran jihohin duk ba su girbe tasu ba. Mutanen  Najeriya muna da yawa doyar jiha guda ba za ta wadatar da mu ba. Hakan ya jawo doyar ta yikaranci. Kuma kin san duk abin da ya yi karanci to fa zai yi tsada” inji shi.

 Har ila yau  Shugaban ya koka game da rashin ciniki da ’yan kasuwar doya ke fama da shi, inda ya alakanta hakan da rashin isassun kudi a hannun jama’a. “A yanzu haka muna fama da rashin ciniki. Duk da cewa doyar ta yi tsada, amma tsadar ba mai yawa ce wacce jama’a za su kasa saye ba. 

A ganina abin da ya jawo hakan rashin wadatar kudi a hannun jama’a sakamakon matsin tattalin arziki da ake fuskanta.  Wallahi rashin cinikin ya dame mu, saboda ita doya kayan gwari ce, kullum farashinta sauka yake. Idan ka kawo doya yau akan Naira dubu 100 idan ba ka samu ka siyar a yau ba, to gobe asara za ka yi  saboda a goben za a kawo sabuwa kasuwar sai ka ga bai fi a saye ta Naira dubu 90 ba.”