Jirage marasa matukan Rasha sun yi wa Ukraine ruwan bama-bamai
Rasha ta kaddamar da harin jirage marasa matuka a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine a safiyar Litinin.
Rasha ta kaddamar da harin jirage marasa matuka a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine a safiyar Litinin.
Tun da misalin karfe 6.30 agogon Ukraine, jirage marasa matuka suka fara yi wa birnin Kyiv luguden bama-bamai, lamarin da ya sa gine-gine da dama kamawa da wuta da kuma hayaki a sassa daban-daban.
- An gano bututun satar mai a kusa da sansanin soji
- Fursunoni 8 ne sun mutu, 57 sun jikkata a gobarar gidan yarin Iran
Fadar Shugaban Kasar Ukraine ta, “Jirage marasa matuka samfurin Kamikaze daga Rasha sun yi kwamba suna luguden wuta a babban birnin kasarmu, wanda suke ganin hakan zai taimaka musu.”
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Ukraine, Andriy Yermak, ya ce, hare-haren sun nuna Rasha ta karaya a yakin da suka shafe wata takwas suna gwabzawa.
Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko, ya ce harin jiragen ya lalata gine-gine a yankin Shevchenkivsky, yana mai kira ga mazauna da su shige mafakar da aka tanadar musu.
“Ma’aikatan kashe gobara suna kokarin kashe wuta a gidaje, wadanda da dama sun lalace, a yayin da jami’an lafiya da gudanar da aikin ceto a yankin.
“Muna kokarin gano mutanen da abin ya ritsa da su,” in ji shi ta shafinsa na Telegram.
Wadanann sabbin hare-hare na zuwa ne mako guda bayan Rasha ta kaddamar da wani gagarumin harin makami mai linzamai a kan birnin Kyiv da sauran sassan kasar Ukraine.