Jirage sun kai hari kan fadar Shugaban Kasar Rasha

Fadar Kremlin ta ce Rasha na da hakkin daukar fansa, amma Ukraine ta nesnta kanta da harin.

Jirage sun kai hari kan fadar Shugaban Kasar Rasha

Rasha ta zargi kasar Ukarine da kai harin bom da jirage marasa matuka a kan Fadar Kremlin a cikin dare.

Fadar Kremlin ta yi zargin harin wani yunkuri ne a kan rayuwar Shugaba Vladimir Putin, duk da cewa Mista Putin bai samu ko rauni ba, haka ma ginin da bom sin ya samu, a harin.

Fadar Kremlin ta ce Rasha na da hakkin daukar fansa a kan harin da ta kira ta’ddanci, inda ta bayyana cewa ta harbo jirage biyun da suka kai harin.

Amma kakakin shugaban kasar Ukraine, Mikhaylo Podolyak, ya ce, “Ukraine ba ta da alaka da harin da aka kai wa Kremlin domin babu wata manufar sojin da haka zai cimma.”

Ya yi zargin Rasha ce ta “kitsa harin domin ta samu dalilin da za ta fake da shi wajen kai harin ta’ddanci a kan Ukraine.”

Kafar yada labarai ta Rasha, RIA ta bayyana cewa Mista Putin ba ya Fadar Kremilin a lokacin da aka kai harin, yana gidansa da ke Novo Ogaryovo, kuma ya ci gaba da harkokinsa yadda aka saba.

Ta kuma bayyana harin a matsahin, “Yunkurin barazana ga rayuwar shugaban kasar a ranar 9 ga watan Mayu da zai halarci Faretin Ranar Nasara.

Kafofin yada labaran Rasha sun tabbatar da harin tare da fitar bidiyon yadda wasu jirage biyu marasa matuka guda biyu suka kai harin bom din a cikin dare.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos