Jiragen dakon kaya tsakanin Najeriya da Saudiyya za su dawo aiki —Keyamo
Ministan jiragen sama ya ce kamfanin Air Nigeria da gwamnatin Buhari ta kafa damfara ce
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a dawo da zirga-zirgar jiragen dakon kaya tsakanin Najeriya da kasar Saudiyya.
Ya sanar da haka ne a lokacin yake jawabi kan ayyukan ma’aikatarsa a ranar Litinin.
Da yake ba da albashir din, Keyamo ya ce, “Harkar jiragen jigilar kaya na samar da sama da Dala tiriliyan shida a duk shekara a duniya.
“A halin yanzu Najeriya na tafka asara a wannan bangaren saboda akwai kasashen da ba ma harkar da su.
- Kotu ta umarci a fitar da Aminu Bayero daga karamar fada
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kauce Wa Cututtukan Masu Yaduwa Da Damina
“Amma ina ba ku albashir da cewa yanzu mun shawo kan wannan matsala,” in ji shi.
Keyamo ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta kammala biyan kamfanonin jiragen kasar waje kudadensu da suka makale a hannunta.
Ya kara da cewa kamfanin jiragen Nigaria Air da aka kaddamar a jajabirin mika mulkin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari tsantsan damfara ce.
Keyamo wanda shi ne karamin ministan kwadago a mulkin Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin Tinubu ta dakatar da aikin Nigeria Airr domin ba komai ba ne face ungulu da kan zabo.
Ana iya tuna cewa tsohon ministan jiragen sama na zamanin Buhari, Sanata Hadi Sirika, yana fuskantar shari’a da hukumar yaki da almundhana (EFCC) bisa zargin karkatar da biliyoyin Naira da ke da alaka da aikin samar da Nigeria Air.
“Kabu kamfanin Nigeria Air kuma ba a taba yin sa ba; kada wani ya yaudare ku. Jirgin kamfanin kasar Ethiopia kawai aka goga wa fentin tutar Najeriya.
“Idan dai tutar Najeiya ce, mene ne dalilin ba wa kamfanin kasar waje a hana na cikin gida damar yawo da fentin tutar kasarmu?
“Idan har kamfanin na Najeriya ne, to dole ya zama na ’yan kasa domin karuwar ’yan Najeriya, ba irin wannan da ’yan kasar waje ke tafiya da kashi 60% na ribar kamfanin ba,” in ji Festus Keyamo.