Jiragen leken asiri na Amurka sun fara shawagi a Najeriya

kasar Amurka ta ba da sanarwar cewa ta fara shawagi da jiragen sama na leken asiri a Najeriya, a matsayin wani yunkuri na ceton ’yan matan nan da aka sace daga makarantar sakandaren Chibok da ke Jihar Borno.An sace ’yan matan fiye da 200 ne daga makarantar ’yan matan da ke garin Chibok a Kudancin […]

Jiragen leken asiri na Amurka sun fara shawagi a Najeriya
Jiragen leken asiri na Amurka sun fara shawagi a Najeriya

kasar Amurka ta ba da sanarwar cewa ta fara shawagi da jiragen sama na leken asiri a Najeriya, a matsayin wani yunkuri na ceton ’yan matan nan da aka sace daga makarantar sakandaren Chibok da ke Jihar Borno.
An sace ’yan matan fiye da 200 ne daga makarantar ’yan matan da ke garin Chibok a Kudancin Jihar Borno fiye da mako hudu da suka wuce.
Wani babban jami’in gwamnatin kasar Amurkar ya ce kasar ta turo jami’an tsaro da kwararru zuwa Najeriya domin su taimaka wajen gano ’yan matan da ’yan Boko Haram suka sace wata guda da ta gabata,
Jami’in ya ce, “Mun yi musayar bayanan hotunan tauraron dan Adam da ’yan Najeriya, kuma jiragen leken asirin suna shawagi a Najeriya bisa izinin gwamnati.”
Kakakin Fadar Shugaban Amurka ta White House, Jay Carney ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan cewa tawagarsu ta hada da wakilai daga Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar da Ma’aikatar Tsaro da Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta FBI da sauran hukumomi na ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.
Ita ma kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Jen Psaki ta shaida wa ani tarin manema labarai a ranar Litinin cewa, Amurka tana samar da bayanan sirri don gano ’yan matan. Kuma jami’an Amurka da ake da su “suna zurfafawa wajen bincike da tsara abubuwa ta hada hannun da gwamnatin Najeriya da kuma abokan hadin gwiwa na kasashen duniya da kawayen Najeriya,” inji ta.
Wasu jami’an Amurka biyu da suka yi magana bisa sharadin a sakaya sunansu, sun ce Amurka tana duba yiwuwar turo jiragen leken asiri marasa matuka domin su taimaka wajen binciken.
daya daga cikin jami’an Amurka ya shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa Amurka tana gudanar da shawagi da jiragen leken asirin marasa matuka “na wasu kwanaki” sai dai bai yi karin bayani ba. A makon jiya karamar sakatariya mai kula da harkokin Afirka Linda Thomas-Greefield ta fadi a wata tattaunawa cewa Najeriya ta bukaci taimakon jiragen leken asiri daga Amurka.