Jiragen ruwa dauke da shinkafar fasakwauri sun isa gabar tekun Kwatano – Kwastam
Hukumar hana fasakwauri ta ƙasa ta sami bayanan sirri da ke nuni da isowar tarin jiragen ruwa maƙare da shinkafa da ‘yan fasakwauri ke yunkurin shigowa da ita kasar nan ta kan iyakar Najeriya da kasar Kwatano, kwanturolar rundunar a Jihar Ogun Sani Madugu ne ya shaida wa ‘yan jarida hakan a ranar Larabar da […]
Hukumar hana fasakwauri ta ƙasa ta sami bayanan sirri da ke nuni da isowar tarin jiragen ruwa maƙare da shinkafa da ‘yan fasakwauri ke yunkurin shigowa da ita kasar nan ta kan iyakar Najeriya da kasar Kwatano, kwanturolar rundunar a Jihar Ogun Sani Madugu ne ya shaida wa ‘yan jarida hakan a ranar Larabar da ta gabata a babban ofishin rundunar da ke Idiroko a Jihar Ogun. Ya ce rundunar ta kwastam ta samar da kudin shiga Naira biliyan 5 da miliyan 800 a cikin watanni 11na shekarar 2017.
Kwanturola Sani Madugu ya kara da cewa akwai bayanan asiri da suka samu na tarin jiragen ruwa maƙare da shinkafa wacce in fasakwabri ke shirin shigowa da ita don haka a shirye suke su cigaba da dakile ayyukan ‘yan fasaƙwauri.
“Yanzu haka muna da shinkafar da muka kama sama da buhu dubu 19 baya ga dubu 12 da za a kai wa ‘yan gudun hijirar rikicin boko haram da ke Jihar Yobe. Wannan lokaci ne na bukukuwan karshen shekara lokaci ne da ayyukan ‘yan fasaƙwauri ke kara kamari. Don haka rundunar mu ba za ta gajiya ba, domin dakile aikace-aikacen su,” inji shi.
Rundunar ta kwastam ta kame motocin 500 ta kuma yi gagarumin kamu, har sau 777 a tsaknin watan 1 zuwa na 11 a bana.
Kwanturola Sani Madugu ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta kwastam a Jihar Ogun ta samu gagarumar nasarar ne biyo bayan karin da hukumar kwastam ta yi musu na sama da mai’akatan ta 300.
“Wannan kari ya ba mu damar cigaba da ayyukan yaki da ‘yan fasaƙwauri a kowane lokaci, safe da dare. Kuma ina tabbatar maka cewa a nan kan iyakar kasa ta Idiroko za mu yi bikin karshen shekara, muna nan mun sanya ido a kan duk wani kaya da za a yiwo fasaƙwaurinsa,” inji shi.