Jiragen ruwa sun yi karo da juna a tekun Jamus

Mutane da dama sun bace bayan wasu jiragen ruwa biyu sun yi karo a kasar Jamus, inda daya daga jiragen ya nutse

Jiragen ruwa sun yi karo da juna a tekun Jamus

Mutane da ba a tantance adadinsu ba sun bace bayan wasu jiragen ruwa biyu suka yi taho-mu-gama a tekun North Sea da ke kasar Jamus.

Hukumomin Jamus sun bayyana fargabar daya daga cikin jiragen ruwan da suka yi karo — dauke da tutar Birtaniya — ya nutse a tekun a sakamakon hatsarin na safiyar Talata.

Hukumar kula da lafiyar teku da kasar Jamus ta ce jiragen ruwa da dama da kuma helikwafta na gudanar da aikin ceto da kuma ciro jirgin da ya nutse, inda aka yi nasarar ceto mutum daya a tekun bayan hatsarin, wanda kuma yake samun kulawar likitoci.

Jirgin da ya nutse mai suna Verity, yana hanyarsa ta zuwa barin Immingham na kasar Birtaniya daga yankin Bremen na Jamus ne iftila’in ya rutsa da shi a Kudu maso Arewacin tsibirin Helgoland.

Dayan kuma mai suna Polesie, ya taso ne daga birnin Hamburg na kasar Jamus zuwa La Coruna da ke kasar Spain.

Hukumar ta bayyana cewa Verity mai tsawon mita 91 (kafa 300) shi ne karami a cikin jiragen da suka yi hatsarin, a yayin da tsawon Polesie ya kai mita 190, kuma yana dauke da mutum 22 a lokacin da hatsarin ya auku.Kawo yanzu dai hukumomi ba su bayyana musabbabin hatsarin jiragen ruwan ba, ko adadin mutanen da ke cikin jiragen ruwan.