Jiragen sama marasa matuka za su fara raba magunguna a Ruwanda
Daga watan gobe ne, likitoci da kuma nas-nas a yankunan karkarar kasar Ruwanda za su fara sayo magunguna ta hanyar aikewa da sakon wayar hannu wato Tes, inda daga bisani jirgin sama mara matuki zai kai musu wurin da suke so.Jiragen za su fara kai magungunan asibitoci ne ta hanyar amfani da manhajar GPS, inda […]

Daga watan gobe ne, likitoci da kuma nas-nas a yankunan karkarar kasar Ruwanda za su fara sayo magunguna ta hanyar aikewa da sakon wayar hannu wato Tes, inda daga bisani jirgin sama mara matuki zai kai musu wurin da suke so.
Jiragen za su fara kai magungunan asibitoci ne ta hanyar amfani da manhajar GPS, inda za su rika mika kunshin magungunan ta hanyar salo irin na saukar lema.
Wani kamfanin kasar Amurka mai suna Zipline ne zai gudanar da wannan aikin, kuma ya ce jiragen za su iya kai kunshin sakonni guda 150 ga cibiyoyin lafiya 21, kamar yadda kafar yada labarai ta Aljazeera ta bayyana.
kasar Ruwanda tana fama da matsalar mutuwar kananan yara wajen haihuwa, inda kashi 58.19 ke mutuwa a cikin kowace haihuwa dubu daya da aka samu, amma mace-macen za su ragu idan wannan sabon tsarin amfani da jirage marasa matuka ya fara aiki a kan lokaci.
Gina asibitoci da kuma tafiyar da su abu mai tsada, amma gwamnatin Ruwanda tana so ta zama kasa ta farko a duniya da za ta fara amfani da irin wannan fasaha a bangaren kiwon lafiya.
Kuma masana suna ganin, idan shirin ya yi nasara, gwamnati za ta ci gaba da amfani da shi a sauran fannonin ci gaban tattalin arzikin kasar.