Jiragen sojin Mali sun ragargaji ’yan ta’adda

Jiragen sojin Mali sun ragargaji ’yan ta’adda a arewacin kasar

Jiragen sojin Mali sun ragargaji ’yan ta’adda

Jirgin sojin saman Pakistan. Hoto: Aljazeera

Rundunar sojan Mali ta ce ta kaddamar hare-hare ta sama kan “kungiyoyin ta’addanci” da ke shirin kai hare-hare a Arewacin kasar.

“Mun ragargaza yan ta’adda a wani harin sama da ta kai kan kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da jagoran su da ake nema ruwa a jallo,” a cewar rundunar ta shafinta na Twitter.

Rundunar sojin ta ce ta lalata wata mota a farmakin, kuma ta gano “kayan kera bama-bamai da alburusai masu yawa”.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan ta’adda sun matsa lamba ga mutanen arewacin Timbuktu, yankin da a karshen watan Agustan masu ikirayin jihadi suka karbe iko da shi.

Tun a shekara ta 2012 ne kasar Mali ta fama da matsalar tsaro da ta faro daga arewacin kasar ta kuma yadu zuwa tsakiyar kasar da ma makwabciyarta Burkina Faso da Nijar.

Gwamnatin mulkin sojan Mali da ta kwace mulki a shekarar 2020, ta ba da fifiko ga diyaucin kasar.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA mai ma’aikav 13,000 da ta fara aikewa Mali a 2013 za ta fice daga kasar nan da karshen shekara bisa bukatar gwamnatin mulkin soja.

Tags