Jiragen yaƙi sun hallaka gomman ’yan ta’adda a Zamfara

Sojojin sun lalata sansanin ‘yan ta’addan tare da kashe wasu.

Jiragen yaƙi sun hallaka gomman ’yan ta’adda a Zamfara

Jiragen Yaƙin Sojin Saman Najeriya, sun yi wa sansanin ’yan ta’adda uku ruwan bama-bama, inda suka hallaka da dama a Jihar Zamfara.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama, AVM Edward Gabkwet, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Gabkwet, ya ce rundunar Operation Hadarin Daji, sun lalata sansanin kasurguman ’yan bindiga da suka hada Abdullahi Nasanda da ke Zurmi, da Malam Tukur a Gusau, da kuma wasu a Karamar Hukumar Maradun.

Ya ce bayan samun bayanan sirri rundunar ta kai hari sansanin Nasanda, inda ’yan ta’adda ke boye makamai da babura.

“Bayan an tabbatar da bayanan da aka samu, an kai harin ne ta hanyar amfani da jiragen sama, inda aka kashe ’yan ta’adda da dama.

“An kai irin wannan farmaki sansanin Malam Tukur, inda aka hangi ‘yan ta’adda.

“Hare-haren da aka kai sun yi sanadiyyar mutuwar ’yan ta’adda da dama tare da ƙone kayayyakinsu.

“An sake kai ire-iren waɗannan hare-haren ta sama a yankin Kanikawa da ke Karamar Hukumar Maradun, inda aka kai hallaka ‘yan ta’adda da makamansu,” in ji shi.