Jiragen yaki sun hallaka shanu 1,500 a kauyukan Fulani

Jiragen yaki sun yi wa shanu luguden wuta a lokacin ake shirin fita kiwo da dabbobin.

Jiragen yaki sun hallaka shanu 1,500 a kauyukan Fulani

Jiragen soji sun hallaka shanu 1,500 bayan sun yi musu luguden wuta a wasu kauyukan Fulani da ke Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba.

Jiragen sojin sun yi wannan luguden wuta ne a yankunan Kashinbila da Tor Donga a ranakun Laraba da Alhamis.

Wani makiyayi a yankin, Sadu Saidu, ya ce daya daga cikin jiragen ya kashe masa shanu 120, da shanun dan uwansa 105 a harin.

“Muna shirin fita da dabbobinmu zuwa kiwo sai muki ji karar jirgin, da zuwansa kafin kiftawa da Bismillah sai ya bude wuta.

“Nan take muka arce muka shige cikin daji muka labe don tsira da rayukanmu; Cikin dan kankanin lokaci da aka yi abin na farko sai da muka kirga shanu kusan 700 da aka kashe,” inji Sadu.

Ya ce washegari wani jirgi ya sake kai hari a wasu kauyukan Fulani inda a nan kuma ya kashe shanu 750.

Shi ma wani Bafulatani a yankin mai suna Musa ya ce bayan shanun da aka kashe, akwai shanu da dama da suka samu raunin harbi, dole suka je aka yi gwanjonsu a kasuwar garin Takum, kafin su kasa.

Musa, wanda ya ce daruruwan Fulani sun fara kaura zuwa yankin kasar Kamaru da garken shanunsu, ya kara da cewa bayan harin, sai da naman shanu ya bazu a kasuwar Takum, wanda dole ake sayarwa da arha saboda yawansa.

Mun yi kokarin jin ta bakin Shugaban kungiyar Fulani ta Miyyetti Allah, a Karamar Hukumar Takum, Alhaji Bello, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Mun yi ta kiran wayarsa, amma bai amsa ba, har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da harin jiragen yakin, amma ya ce a Jihar Binuwai abin ya faru, ba Jihar Taraba ba.

“Abin kai ya faru ne a Jihar Binuwai ba a yankin Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba ba, kamar yadda DCO na yankin Takum ya shaida min” inji shi.