Jirgi ya jefa wa masu taron Mauludi bom a Kaduna
Ana fargabar harin bom din jirgin sojin ya hallaka mutane sama da 30 a wurin taron Mauludi a kusa da filin jirgin sama na Kaduna
Wani jirgin soji ya jefa bom a kan masu taron Mauludi a yankin Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne a misalin karfe 9 na daren Lahadi a yankin da ke kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna.
Wani mazaunain yankin ya ce “mutane na cikin bikin Mauludi kawai sai jirgin sama ya jefo masu bom wanda ya yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30 a wurin,” inji shi.
Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa akwai yiwuwar hasarar rayukan ya karu.
- Gwamnati ta sa jirgin Shugaban Kasa a Kasuwa
- Kano: Lauyoyin Arewa 200 sun lashi takobin taimakon Abba a Kotun Koli
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki bayyana yawan wayanda suka rasa rayukansu ba.
Amma ya ce za su sanar da manema labarai abin da ya faru a wurin bayan sun yi taron gaggawa na majalisar tsaron jihar.