Jirgin babban hafsan sojin Libya ya yi batan dabo a Turkiyya
Jirgin ya nemi izinin yin saukar gaggawa kafin daga bisani a daini jin duriyarsa
Jiragen sama a filin jirage na Ankara
Hukumomi sun sanar cewa an rasa layin sadarwa da jirgin da ke dauke da Babban Hafson Sojin Libya, Mohammed Ali Ahmed al-Haddad, a kusa da Ankara, babban birnin kasar Turkiya.
Turkiyya ta bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan jirgin ya nemi izinin yin saukar gaggawa, lamarin da ya sa aka fargabar game da halin da jirgin da mutanen cikinsa ke ciki a tsakanin kasashen biyu.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya ta sanar cewa jirgin yana dauke da wasu mutun hudu bayan Babban Hafsan Sojin na Libya.
Ministan ma’aikatar, Ali Yerlikaya, ya ce, jirgin kirar Falcon 50 yana hanyarsa ta komawa birnin Tripoli na kasar Libya daga Ankara ne lokacin da aka daina samun layin sadarwa da shi.
- Cin zarafin Kansila ya jefa hadiman gwamna a matsala a Gombe
- NDLEA ta kama mutum 143 da miyagun kwayoyi kilo 982.8 a Sakkwato
Jirgin da ke kan hanyarsa daga Ankara zuwa Tripoli ya nemi izinin sauka ta gaggawa yayin da yake kan yankin Haymana na Ankara, amma daga baya ba a sake jin duriyarsa ba.
Bayanan bin diddigin jiragen sama sun nuna cewa an karkatar da wasu jirage daga filin jirgin sama na Esenboga da ke Ankara.
Duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da ko jirgin ya yi hatsari ba, wani bidiyo a tashoshin talabijin na Turkiyya ya nuna wani walƙiya a wurin da aka ce jirgin ya rasa layin sadarwar rediyo.
Zuwa yanzu dai ba a samu wani jawabi kai tsaye daga hukumomin Libya ba.
Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta bayyana a farkon makon nan cewa Babban Hafsan Sojojin Libya ya kai ziyara Ankara, inda ya gana da takwaransa na Turkiyya da wasu manyan kwamandojin soja.
Turkiyya na da kusanci da gwamnatin Libya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita, inda take ba ta tallafin tattalin arziki da na soja.