Jirgin Chadi ya fara zirga-zirga a Kano
A ranar Litinin din makon Jiya ce jirgin kasar Chadi ya fara sauka a Jihar Kano. Jirgin wanda ya taso daga birnin Ndjamena zuwa Kano ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin karfe 4:00 na yamma. Darakta-Janar na Kamfanin Tchad Airline, Mista Wssihun Asres Tiruneh ya bayyana cewa […]
A ranar Litinin din makon Jiya ce jirgin kasar Chadi ya fara sauka a Jihar Kano.
Jirgin wanda ya taso daga birnin Ndjamena zuwa Kano ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin karfe 4:00 na yamma.
Darakta-Janar na Kamfanin Tchad Airline, Mista Wssihun Asres Tiruneh ya bayyana cewa wannann rana ce mai matukar tarihi ga kasashen biyu duba da samun jirgin da ya sake hada kasashen biyu, bayan daukar shekaru sama da goma ba tare da samun zirga-zirga tsakaninsu ba. “Sama da shrkaru goma ke nan tun daga lokacin da jirgin farko na kasar Chadi ya daina gudanar da zirga-zirga. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga kasashen biyu.”
Darakta-Janar din ya kuma kara da cewa sun zabi yin zirga-zirga a Jihar Kano ne duba da kasancewarta cibiyar kasuwanci a Najeriya.
A cewarsa, jirgin zai rika zirga-zirga a Jihar Kano sau daya a mako, inda ya yi alkawarin kara fadada zirga-zirgar jirgin sau uku a mako daga watan gobe.
Shi ma a nasa jawabin, Janar-Manajan Hukumar da ke Kula da Tashar Jiragen Sama ta Kasa, Alhaji Bello Muhammad Sabo, ya yi alkawarin bayar da duk wani taimako da jirgin ke bukata daga hukumarsa, inda kuma ya nemi jirgin da ya tabbatar ya yi duk abin da ya dace wajen biyan bukatun abokan huldarsa.