Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya
Ana sa ran jirgi na biyu ya tashi ranar Litinin
Wasu maniyyata Aikin Hajji
Jirgin farko dauke da mainiyyatan Jihar Gombe su 508 ya tashi daga filin jiragen sama na kasa da kasa da ke garin Lawanti a Jihar Gombe zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da Aikin Hajjin bana.
Ana sa ran jirgin kai tsaye zai wuce filin jirgin saman Sarki Abdulazeez da ke Jidda a kasar ta Saudiyya.
- Gurgu mai hawan gado da kyar ya hau saman ‘Burj Khalifa’ gini mafi tsawo a duniya
- Mutum 17 sun mutu a wajen sharholiya a Afirka ta Kudu
Maniyatan ana sa ran daga birnin na Jiddah za su wuce zuwa birnin Madina don gudanar da ziyarya a Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W.)
Jirgin na kamfanin Max Air ya tashi ne a ranar Lahadi.
Mahajjatan za su yi kwanaki biyar ne a Madina kafin su wuce zuwa birnin Makka kafin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan
Ana sa ran jirgi na biyu zai tashi da wani rukunin maniyyatan a ranar Litinin mai zuwa.