Jirgin hatsi na farko daga Ukraine ya isa masaukinsa
Wani jirgin dakon kaya dauke da masara daga Ukraine ya isa kasar Turkiyya, inda ya zama jirgin ruwa na farko da ya isa inda ya nufa tun bayan da aka kulla yarjejeniyar sakin kayan abinci da suka makale a tashoshin ruwan tekun Baharul Aswad, tun bayan yakin. Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ce jirgin ruwan […]
Wani jirgin dakon kaya dauke da masara daga Ukraine ya isa kasar Turkiyya, inda ya zama jirgin ruwa na farko da ya isa inda ya nufa tun bayan da aka kulla yarjejeniyar sakin kayan abinci da suka makale a tashoshin ruwan tekun Baharul Aswad, tun bayan yakin.
Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ce jirgin ruwan Polarnet mai dauke da tutar Turkiyya ya isa Kocaeli da ke gabar tekun Marmara a ranar Litinin.
- Akwai yiwuwar ninka kudin kiran waya da data a Najeriya
- Akwai yiwuwar ninka kudin kiran waya da data a Najeriya
Kawo yanzu, jiragen ruwan hatsi 10 ne suka tashi daga tashar jiragen ruwa na Ukraine, a cewar ma’aikatar tsaron Turkiyya.
Jirgin Razoni shi ne ya fara tashi daga Ukraine zuwa Lebanon a ranar Litinin din makon jiya, sai dai kuma an samu jinkirin isarsa.
An ci gaba da jigilar kayayyaki ne bayan yarjejeniyar da aka cimma a watan Yuli na sakin miliyoyin ton din hatsi da aka tare a tashoshin jiragen ruwa na Ukraine, kasa mai mahimmancin samar da abinci da aka fi sani da kwandon burodi na Turai.
Ana ganin jigilar kayayyakin yana da mahimmanci don daidaita farashin hatsi a kasuwannin duniya a yayin da ake fargabar yunwa a yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka.
A karkashin yarjejeniyar, Ukraine ta yi alkawarin jagorantar jiragen ruwa a cikin ruwan da aka gano nakiyoyi, ita kuma Rasha ta yi alkawarin ba za ta kai hari kan jiragen ruwa da wasu kayayyakin more rayuwa na tashar jiragen ruwan Ukraine ba.
Wadanda suka jagoranci kulla yarjejeniyar — Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya — suna taimakawa wajen sanya ido kan jigilar kayayyaki don tabbatar da cewa jiragen ruwa ba sa safarar makamai zuwa yankin da ake yaki.
Fiye da ton miliyan 20 na hatsi daga girbin bara na ci gaba da jiran fitar da su zuwa kasashen waje, in ji hukumomin Ukraine a farkon wannan watan.