Jirgin kasa ya fara jigilar kaya daga bakin tekun Legas zuwa Kano

An fara jigilar kwantainan kayan da aka shigo da su daga kasashen waje zuwa Kano daga bakin tekun Apapa da ke Legas

Jirgin kasa ya fara jigilar kaya daga bakin tekun Legas zuwa Kano

Titin jirgin kasa. (Hoto: adobestock)

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da jigilar kaya daga tashar ruwa ta Apapa da ke Legas zuwa tashar kan Tudu da ke Dala a Kano.

Ministan Sufuri Sa’idu Ahmed Alkali ne ya jagoranci taron kaddamar da jirgin kasa a tashar kan Tudu ta Dala, inda ya jaddada gagarumin tasirin da hakan zai yi kan harkokin kasuwanci musamman a Arewacin Najeriya.

Alkali ya bayyana mahimmancin aikin wajen saukaka shigo da kaya da fitar da su kasashe waje, wanda hakan ya kawo sauki ga harkokin kasuwanci a Arewa.

Ya bayyana kudirin gwamnati na bunkasa hanyoyin sufuri na zamani da kuman inganta tsaro mai dorewa, tare da amincewa da sufuri a matsayin wani muhimmin bangare na ci gaban tattalin arziki.

Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnati ta samu wajen samar da kudade don gudanar da muhimman ayyukan layin dogo da suka hada da kammala aikin Kaduna zuwa Kano da kuma aikin gina layin dogo na Kano zuwa Maradi da ake yi.

Manajan daraktan tashar ta Dala, Ahmad Rabiu, ya ce aikin jirgin kasa zai sanya Kano zama babbar cibiyar tantance kaya da fitar da su zuwa kasashen waje.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam ya wakilta, ya yaba da shirin, inda ya ce hakan zai taimaka matuka wajen inganta matsalolin sufuri da ’yan kasuwa ke fuskanta a yankin, musamman idan aka lura da halin rashin kyau da titunan kasar suke ciki.

Firimiya: Manchester United da Chelsea sun yi kunnen doki

Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci a ranar Litinin

Da ni ne mulki a Najeriya da ba ta shiga tasku ba — Atiku

Bayan hukuncin CAF an fara kamen ’yan Najeriya a Libya