Jirgin kasa ya kashe wani kurma a Legas

’Yan gwangwan da ke harkokin kasuwanci a bakin titin dogo da ya ratsa unguwar Agege sun ga tashin hankali lokacin da  jirgin kasa ya buge wani kurma mai suna Abdullahi Kurma, ya yi rugurugu da kafarsa ta dama, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Muhammed Lawan […]

Jirgin kasa ya kashe wani kurma a Legas

Marigayi Abdullahi Kurma lokacin da yake raye.’Yan gwangwan da ke harkokin kasuwanci a bakin titin dogo da ya ratsa unguwar Agege sun ga tashin hankali lokacin da  jirgin kasa ya buge wani kurma mai suna Abdullahi Kurma, ya yi rugurugu da kafarsa ta dama, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna Muhammed Lawan ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne yayin da Abdullahi, mai kimanin shekaru 45, ya zo tsallaka titin jirgin. “Muna zaune, sai muka ga wani mutum ya zo tsallaka titin jirgi, to a lokacin jirgin ya zo daf da wurin, sai mutane suka yi ta yi masa ihun ‘ga jirgi nan’, shi kuwa saboda kurma ne, bai ji abin da suke fadi ba. Yana tsallakawa, sai kan jirgin ya buge shi ya take masa kafar dama, nan take ta gutsure, wuri ya yi kace-kace da jini, aka kai shi asibiti. Daga bisani aka ce ya mutu”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “A lokacin da abin ya faru mutane sun ji haushin mutumin sosai, domin da yawa sun yi ta yi masa kururuwar ‘ga jirgi nan’, amma bai ji ba, daga bisani da mutane suka gano kurma ne, sai kowa ya tausaya masa. Gaskiya hankalina ya tashi sosai saboda ban taba ganin irin wannan ba a shekaru 10 da na yi a nan ina sana’a”.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don ji ta bakin hukumar lura da jiragen kasa, reshen jihar Legas, ya ci tura domin jami’an ma’aikatar sun ce ba su da hurumin yin magana da manema labarai.
Sai dai daya daga cikin jami’an hukumar, wanda ya so a saka sunansa, ya ce kusan daga lokaci zuwa lokaci sai hukumar ta sami labarin jirgi ya buge wani ko kuma fasinjojin da ke hawa samansa sun fado. Sai dai mutane ne ke jawo wa  kansu, domin yadda suke wasa da jirgin wajen tsallaka titinsa da kuma hawa samansa duk da kokarin da hukumar ke yi na fadakar da jama’a hadarin da ke tattare da yin haka.
Jami’ai a  ofoshin ’yan sanda na unguwar Isekoko, kusa da inda lamarin ya auku, ba su yi karin bayani kan lamarin ba, amma majiyar da ke kusa da ofishin ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ’yan sanda sun je wurin don daukar bayanan abin da ya auku.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas ya ci tura.
Dangin Abdullahi, wanda ba shi da aure sai mahaifiyarsa da ’yan’uwansa maza da mata, wadanda ke zaune a unguwar Agege sun bayyana cewa suna tuntubar juna domin daukar mataki na gaba kan batun.
Makwabtansa sun bayyana shi da mutum mai kokarin neman na kansa, wanda ba shi da girman kai a kan sana’a domin samun kudin kashewa.