Jirgin kasa ya markade almajirai uku a Zariya

A ranar Asabar ce wani jirgin kasa na daukar kaya ya markade wasu almajirai uku a Zariya. Wani dan agajin kungiyar Jama’atu Nasril Islam mai suna Salisu da lamarin ya faru a gabansa kuma suka yi aikin tattara gawawwakin almajiran ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 1:00 na rana ne jirgin kasan wanda […]

Jirgin kasa ya markade almajirai uku a Zariya
Jirgin kasa ya markade almajirai uku a Zariya

A ranar Asabar ce wani jirgin kasa na daukar kaya ya markade wasu almajirai uku a Zariya. Wani dan agajin kungiyar Jama’atu Nasril Islam mai suna Salisu da lamarin ya faru a gabansa kuma suka yi aikin tattara gawawwakin almajiran ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 1:00 na rana ne jirgin kasan wanda ya fito daga babban tasharsa ta Zariya ya ratsa Unguwar Gabari a Tudun Jukun, kuma a daidai wani hawa sai taragonsa biyu suka yanke ya yiwo baya a guje, jama’a suka rika gudu amma almajiran ba su ankara ba, jirgin ya markade su.
Malamin almajiran mai suna Malam Ibrahim ya bayyana wa Aminya cewa, “Yaran da jirgi ya taka almajiraina ne kuma ’ya’yan ’yan uwa ne da suka kawo su domin koyon karatu; babbansu shi ne Nazifi mai shekara 14 , sai Aminu mai shekara 13 sai kuma Usama mai shekara 12. Tunda nake zaune a wannan unguwa tsawon shekara 30 a lokacin jirgi na zirga-zirga sosai ba kamar yanzu da ba shi sosai ba, ba mu taba ganin irin wannan tashin hankali ba. Kuma ku san saboda sabo ko dabbobinmu da sun ji karar jirgin na zuwa za ka ga duk sun gudu, wannan tsinkewa ya yi don haka ya zo ne shiru, Allah Ya takaita ne da ya tsaya a kan yara uku domin tun daga inda ya tsinko sai da ya koma tasha kuma wadannan wurare duk na zirga-zirgar jama’a ne.”
Game da ko akwai abin da yake bukata daga hukumar jiragen kasa sai ya ce “Ka san yadda lamarin yake wa zai iya ja da gwamnati, sai dai kawai idan ta ga ya dace ta yi wani abu na kawo gyara ko kwantar da hankali sai mu ce mun gode, amma dai duk abin da za a yi rai dai ba haka ya so ba.”
Wani babban jami’in hukumar kula jiragen kasa mai suna Abdullahi Muhammed ya  shaida wa Aminiya cewa jirgin ya tashi da kaya daga tasharsu ta Zariya n zuwa Kaduna amma bayan ya yi tafiyan kilomita sai biyu daga cikin taragun kaya suka yanke suka dawo baya, “To tunda yankewa suka yi kafin a shawo kansa da wahala kuma mun baza jami’anmu ta inda duk jirgin zai bi domin mu kare faruwar haddura. Bayan jirgin ya dawo tasha mun tare shi ne muka ga jikinsa da jini da nama, alamun ya yi barna a baya, inda muna bincike muka ji yara uku ya taka, mun halarci inda abin ya faru tare da ’yan sanda aka yi jana’iza da mu kuma muka jajanta musu sannan muka gayyace su kan su zo ofishinmu a ranar Litinin.
Ya ce za su kafa kwamiti don bincikar abin da ya jawo aukuwar haka. Kuma ofishin’yan sanda na tashar jiragen kasa na Zariya ya tabbatar da faruwar hadarin.