Jirgin kasa ya markade shanu 52 a Kaduna
Akalla shanu 52 ne jirgin kasa da ke zirga-zirga a tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya hallaka a ranar Lahadin da ta gabata a kusa da garin Jere. A cewar ’yan sanda, lamarin ya auku ne da misalin karfe 11:45 na safe lokacin da jirgin ke hanyarsa ta komawa Abuja. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Ahmad […]

Akalla shanu 52 ne jirgin kasa da ke zirga-zirga a tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya hallaka a ranar Lahadin da ta gabata a kusa da garin Jere.
A cewar ’yan sanda, lamarin ya auku ne da misalin karfe 11:45 na safe lokacin da jirgin ke hanyarsa ta komawa Abuja.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahaman ne ya sanar da haka, jim kadan bayan ya ziyarci wurin da abin ya faru.
Kwamishinan ya kuma musanta zargin da wadansu ke yi, cewa wai yan ta’adda ne suka yi kokarin kifar da jirgin domin yin sata. Ya ce masu dabbobin na kan hanyarsu ce ta yin hijira zuwa yankin Funtuwa a Jihar Katsina lokacin da hadarin ya auku.
Ya tausaya wa wadanda suka rasa dabbobin nasu, inda ya ce akwai bukatar su rika kiyayewa tare da kauce wa hanyar jirgi a yayin tafiya da dabbobi cikin daji. “Lamarin ya auku ne a kusa da wani kauye da ake kira Kasarami a kusa da Jere kuma makiyayan na kan hanyarsu ce ta yin hijira zuwa Funtuwa da ke Jihar Katsina. Kuma an ce sai da suka tambaya ko jirgi na bin hanyar dogo a ranar Lahadi amma sai manoman da ke wurin suka ba su bayanin karya, cewa jirgi ba ya wucewa a ranar Lahadi,” inji shi.
“Da muka samu labarin aukuwar hadarin, na aika da jami’ai cikin gaggawa domin kauce wa karya doka da oda. Na kuma gayyaci sarakunan yankin da shugabannin matasa da na manoma, domin tattauna yadda za a ci gaba da zama lafiya,” inji shi.
Kwamishinan ya kuma musanta tare da jan kunnen masu yada labarun karya a shafukan sada zumunta dangane da hadarin da ya auku, cewa su daina yada labarin da ba su sani ba. Ya ce duk wanda aka kama yana ba da labarin karya domin razana mutanen gari, zai dandana kudarsa.