Jirgin kasa ya murkushe tirelar dangote a Nasarawa
A safiyar Juma’a da ta gabata ne wani jirgin kasa dauke da fasinjoji 210) ya murkushe wata tirelar dangote mai Lamba Kogi AJ 426 dA da lambar kamfanin siminti na Obajana, OBJ.4A.011, a kauyen Gudi da ke karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa. Lamarin wanda ya auku da misalin karfe 9:10 na safe jirgin ya […]
A safiyar Juma’a da ta gabata ne wani jirgin kasa dauke da fasinjoji 210) ya murkushe wata tirelar dangote mai Lamba Kogi AJ 426 dA da lambar kamfanin siminti na Obajana, OBJ.4A.011, a kauyen Gudi da ke karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa. Lamarin wanda ya auku da misalin karfe 9:10 na safe jirgin ya yi falle-falle da tirelar amma babu hasarar rai.
Matukin jirgin, Mista James Ogoche ya ce ya fito Kano zuwa Fatakwal ranar Alhamis, kuma a tsarin tukin jirgin kasa idan ka doso inda titin mota ya ketare ko wurin hada-hadar jama’a sai a yi hon don sanar da mutane, kuma ya fara hon din tun kimanin kilomita uku kafin ya kawo Gudi inda hanyar dogo ta ketare titin mota.
Direban ya ce babu zato babu tsammani sai ya ga tirela ta gicciye titin kuma kafin nan take ya gan shi kusa da tirelar dabara ta kare, hakan ya sa ya daki tirelar ta yi falle-falle ya wuce kafin ya samu nasarar tsayawa.
Abba Maliki matukin tirelar ya ce, ya dauko siminti ne daga Obajana zuwa Jos, kuma kafin ya kawo Gudi ya ji motar tana dan yin rikici sai ya ce idan ya kai Jos zan gyara ta kafin ya dawo, amma sai ya ji motar na kokarin tsayawa da kanta. Ya ce da ya zo titin dogon ya dan shiga gargada ne sai ta mutu ya yi kokarin ta tashi amma ta ki, kuma yana kokarin yadda motar za ta bar titin dogon kafin wani abu ya faru, amma bayan minti 15 da tsayuwarta sai ya ji hon din jirgin kasa. “Da na daga kai sai na hango jirgin na zuwa da gudu hakan ya sa na tashi ina daga masa hannu don ya tsaya ashe jirgi ba ya iya tsayawa kamar mota da na ga jirgin yana ta zuwa babu alamun tsayawa sai kurum na ga ya daki motata ya yi falle-falle da ita, sai na sa hannu a kai na fara kuka domin ba ni da wani zabi face rungumar kaddara. Kuma abin da ya fi ba ni haushi shi ne yadda barayin siminti marasa imani da faruwar hadarin suka fara kwashe simiiti kiri-kiri muna hana su, amma suna ki. Na yi ihu har na gaji babu wanda ya kula ni,” inji shi.
Wani dan sanda da ya halarci wuri da hadarin ya auku mai suna Sufeto A.I. Biam ya ce sun samu rahoton aukuwar hadarin, amma har zuwa lokacin ba su tabbatar da wane ne mai laifi ba.