Jirgin kasa ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki

Jirgin kasa wani tarihi ne na sufiri, wanda Turawan  Yamma suka kafa tun sama da karni da ya gabata.  Saboda da muhimmancin sufirin jirgin kasa shi yasa wani fasihin mawaki a kasar Hausa ya wake jirgin kasa,  a inda ya yi masa lakabi da sakaka manyan Turai. Tun kafin zuwan Turawa wani abin ban sha’awa, […]

Jirgin kasa ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki
Jirgin kasa ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki

Jirgin kasa wani tarihi ne na sufiri, wanda Turawan  Yamma suka kafa tun sama da karni da ya gabata.  Saboda da muhimmancin sufirin jirgin kasa shi yasa wani fasihin mawaki a kasar Hausa ya wake jirgin kasa,  a inda ya yi masa lakabi da sakaka manyan Turai. Tun kafin zuwan Turawa wani abin ban sha’awa, Bahaushe ya yi fice a fagen fatauci, a lokacin ana amfani da jakuna ko alfadarar wajen fataucin kayayyakin masarufi, wadanda suka hada da KANWA da GORO da FATU da KABA da GISHIRI, da sauransu, amma da zuwan Turawan  mulkin mallaka  sai al’amura suka canza aka kawo sabon salon abin fatauci na amfani da jiragen kasa cikin sauri da sauki, ba tare da fargabar ’yan fashin da ke cikin tsakiyar daji ko kuma lalacewar abin masarufin.
Hakika zuwan jirgin kasa Arewa ba karamin kawo ci gaba ya yi wajen bunkasa tattalin arziki, musammanma ga fatake masu safara, kowa ya san  manufar  ’yan mulkin mallaka na Turawan  Yamma, domin kawai su wawushe arzikin karkashin kasa da Allah Ya hore wa kananan kasahe don haka lokacin da Turawan  mulkin mallakar Birtaniya suka iso gabar tekun Lagas, sai suka fara kokarin fara hada-hadar dibar albarkatun kasa, don haka  sai aka kaddamar da gina titin jirkin kasa na farko a Najeriya a shekarar 1898  daga IDDO ( LAGOS) zuwa OTTA (OGUN), mai tsawon kilomita 32 wannan hanyar jirgi kasa mai saukin safara da kuma takaita tafiya mai dogon zango, ta saukaka tafiya da jirgin kasa ya kawo da kuma saukin isar albarkatun kasa ga gabar ruwan tekun Legas tasa Turawan  mulkin mallaka shimfida hanyoyin dogo a sassan kasar nan.
Abin lura a nan shi ne za ka ga duk inda layin dogo ya yada zagon imma garin matattarane na harhada amfanin gona ko wajen hada hadar arzikin karkashin kasa na ma’adanai. Turawan  mulkin mallaka suka kara gina wani titin dogon 1901 daga IBADAN ZUWA JABBA mai tsahon kilomita 295, sai kuma aka kara kaddamar da gina wani titin a 1907-1911 daga KANO ZUWA BORNO, sannan sai kuma 1909-1915 JABBA ZUWA MINNA. Sai daga ZARIA IZUWA KAFANCHAN daga nan ya karkare izuwa JOS. Wadannan tituna da na zayyano su ake kira da suna (WESTERN LINE), wato layin dogo na bangaren yamma. A daya bangaren titin dogo ya fara daga Fatakwal da  Aba da Umuahiya da Enugu da Markudi da Lafiya. Da Kafanchan da Bauchi da Gombe da Pataskum, kana ya karkare a Maiduguri wannan shi ake kira da (ESTERN LINE)  wato layin dogo daga gabashi.
A karni na 19 zirga zirga jiragen kasa ta kawo ci gaba masu muhimmaci ga tattalin arzikin kasa. Arewa ta bunkasa ta kai kololuwa ga arzikin kasa.  Hakan tasa gwamnatin wancan lokacin ta ’yan mulkin mallaka suka rika samun saukin kwasar albarkatun kasa ta hanyar layin dogo, hatta kasafin kudi an dogara ne daga arzikin dake Arewa. kididdiga ta nuna cewa a wancan lokacin, hukumar zirga-zirgar jiragen kasa (NRC) ta nuna cewa a shekarar 1964, saboda bunkasar jirgin dogo ta kai fasinjoji masu zirga-zirga a cikinsa 11,288,00. bangaren dakon kaya kuwa ton miliya biyu da dubu 960 jirgin ke daukar kaya, amma a shekarar 1974 sai shiga jirgin da dakon kaya ya ragu a yayin da safarar mutane ta tsaya a 4,342,000 dakon kaya ya koma ton miliyan daya da dubu 98, amma a shekarar 1978 sai yawan fasinjoji ya kara karuwa izuwa miliyan guda da dubu 700, inda a shekarar 1984 ya kai miliyan 15 da rabi. Wannan jimilar yawan fasinjoji ta kai yasa hukumar kula da jiragen kasa (NRC) ta mallaki ma’aikata dubu 45,000 da locomotibes guda 200 da shunters 480 da kuma taragwai na daukar kaya guda dubu  hudu da 900.
Duk da irin tagomashin da jirgin kasa ya bai wa harkar sufiri ta bunkasa fatauci a saukake tsakanin Arewa da kudu, amma sannu a hankali sai harkar jirgin kasa ta fara ja da baya, saboda sakaci irin na shugabanninmu da suka gabata, a lokacin ma’aikata da suka kai sama da dubu 45, sai jimlarsu ta koma dubu 500, bayan  an sallami sauran saboda hukumar ta durkushe kodayake dole a yaba wa gwamnatin SANI ABACHA,  domin ta yi wani namijin kokari,  abin farin ciki da ya faru mai kamar mafarki ga ’yan Najeriya, a ranar 21 ga December 2012, Jirgin ya tashi daga Legas da karfe 11;00 (Am) na safe ya isa Kanon Dabo da karfe 9;00, na dare a tsahon awa 34 da ya yi  yana tafiya. Lallai talakan Najeriya zai sa ran cewa Gwamnatin Najeriya ta fara cika alkawarin da take yi wa talakawanta akan garanbawul a harkar sufurin jirgin kasa, domin bin sahun kasahen kawayenta masu tasowa, wadanda aka yi wa hasashen samun ci gaba mai ma’ana, kuma cikin gaggawa a kankanin lokaci, wadannan kasashe da aka yi wa hasashen cigaba,  tuni sun yi nisa wajen ci gaban fasaha wacce takai kololuwa, a yayin da Najeriya aka barta da tsofaffin matattun jirage masu shekara sama da 50, su kuwa yanzu kasahen tuni sun yi nisa wajen kera jirage masu gudu a karkashin kasa ko kuma masu amfani da wutar lantarki,  kai!
Yanzu an fara gwada wani jirgi mai gudu kamar walkiya a kasar CHINE, mai gudun kilomita300 a cikin awa daya wanda ya tashi daga  BEIJING izuwa SHANGHAI ko wanda aka kaddamar a kasar JAPAN wanda ada ya kanyi minti 90 daga TOKYO izuwa NAGOYA, ya koma minti 40, irin wannan ci gaba da kasashe masu tasowa suka yi fice a faannonin kirkirar kimaya da fasaha, to ya zama dole shugabanninmu a Najeriya da su daure su kawo tsare-tsare, domin mu samu mu zama daya daga cikin kasashe masu bunkasa kimiya da fasaha a wannan karni, amma a zahirin gaskiya sai shugabanninmu sun kau da siyasa aduk lokacin da’aka samu sauyin shugabanci. Akwai bukatar a samu jajirtaccen mutum kamar ministan sufiri nayanzu SANATA ABDULLAHI IDRISS da yayi tsayin daka yaga jirgi kasa ya farfado.
Farfado da jirgin dogo zai kawo ingantuwar hanyoyimmu, domin manyan motocin dakon kaya za su ragu a manyan tituna a samu raguwar cunkushewar tituna, kana rasa rayuka za su ragu. A gefe guda kuwa matasa za su samu ayyukan yi wajen kara daukar ma’aikata, a tashoshin jiragen hada-hada.Leburori tare da kananan ’yan kasuwar da ke tashar, su ma direbobin da ke dakon kaya kakarsu ta yanke saka. Ka ga kuwa direbobin manyan motoci sai su dawo kananan motoci irin su kanta maimakon su bar harkar kwatakwata.
Kafin in karkare wannan mukalar tawa, ya kamata shugabanni a Najeriya su dauki darasi a kan manyan injinan da aka yo oda, domin kafa sabuwar tashar wutar lantarki a KADUNA, amma aka kasa kawo su saboda ba motar da zata iya dakonsu saboda nauyi, a yanzu haka kayan suna ONNE PORT da ke Fatakwal, suna jira a kammala sabuwar hanyar jirgin kasa daga LOKOJA izuwa ABUJA ta karkare a KADUNA.
Za a iya samun Ado Musa Unguwar kaura Goje, Kano a 08069186916

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50