Jirgin Kasan Abuja-Kaduna ya yi hatsari a cikin daji
Sawun farko na jirgin ya yi hatsari a dokar daji inda wasu taragoginsa suka sauka daga kan layin dogo
Sawun farko na jirgin kasa da ke jigilar fasinja daga Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari a cikin dokar daji.
Jirgin da ke dauke da fasinjoji ya yi hastari ne a yankin Jere, kimanin awa daya bayan ya taso daga Kaduna zuwa Abuja a safiyar Lahadi.
Akalla taragogi uku na jirgin ne aka tabbatar sun sauka daga titin jirgin kasa, lamarin da ya tilasta masa tsayawa a cikin dajin.
Hakan kuwa ya faru ne kimanin awa guda bayan tasowan jirgin kasan daga Kaduna a hanyarsa ta zuwa Abuja.
- Akwai barazanar kai wa Majalisar Kano hari —’Yan Sanda
- Rikicin Masarautu: Gwamnatin Kano ta ba wa Ribadu hakuri
- NAJERIYA A YAU: Kura-Kuran Da Abba Ya Tafka A Dambarwar Sarakunan Kano
Zuwa lokacin hada wannan labari dai ana kokarin gyara jirgin da mayar da shi kan layin dogo ya ci gaba da tafiyarsa.
Haka zalika jami’an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro.