Jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki ranar Litinin

Gwamnati ta ba da tabbacin kubutar da fasinjojin jirgin kasan da aka yi garkwua da su

Jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki ranar Litinin

Jirgin kasa

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin ci gaba da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna daga ranar Litinin 23 ga watan Mayu da muke ciki.

Kakakin Hukumar Zirga-zirgar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Mahmood Yakub, ne ya sanar da umarnin daga Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya a ranar Litinin.

Gwamntin ta shaida wa iyalan fasinjojin jirgin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su cewa “Mun dauki batun kubutar da su da matuka muhimmanci; kada a dauki dawo da sufurin jirgin kasan a matsayin rashin kulawa da halin da suke ciki.”

Hakan na zuwa ne kimanin kwana 45 bayan harin bom da ’yan bindiga suka kai wa jirgin kasan a ranar 28 ga watan Maris, suka kashe fasinja 10, suka sace akalla 60, tare da jikkata wasu da dama.

A cewar gwamnatin, tana aiki ka’in da na’in domin ganin an sako fasinjojin ba tare da komai ya same su ba, amma ta ki yin karin bayani saboda abin da ta kari ‘muhimman dalilan tsaro’.
NRC ta bai wa matafiya tabbacin samun karin tsaro a hanya da kuma cikin jirgin, “Ba wai ga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba kawai, har ga daukacin fasinojojin jirign kasa,” inji sanarwar da Yakub ya fitar.

Don haka ya bukaci matafiya su ba da hadin kai ga sabbin matakan da aka dauka domin inganta tsaro a harkar sufurin jirgin kasa.

Sauran sabbin matakan da ya ce an dauka sun hada da karbar lambar shaidar dan kasa ta NIN, takardar shaida mai dauke da hoto, lambar waya, lambar dan uwa ko makusanci, da kuma sauran bayanan fasinja.

Don haka ta shawarci mutane da su guji sayen tikicin jirgi ta barauniyar hanya.