Jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo ranar Litinin
Sawun farko zai bar Tashar Idu da ke Abuja karfe 9:45 na safiya
Gwamnatin Tarayya ta sake sanar da cewa jirgin kasan Abuja-Kaduna zai ci gaba da jigilar fasinja daga ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 da muke ciki.
A ranar Alhamis, Shugaban Hukumar Jiragen Kasa (NRC) Fidet Okhiria, ya sanar cewa an kammala duk shirye-shiryen da suka kamata domin ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasan.
Sai dai sabanin yadda a baya sawun farko na jiragen ke yin sammako, Okhiria ya ce, “AK 1 zai tashi daga Tashar Idu karfe 9:45 na safe ya isa Rigasa 11:53; KA 2 zai bar Rigasa 8:00 ya isa Idu 10:17; “AK 3 ya baro Idu 15:30 ya isa Rigasa 17:38; sai KA 4 ya tashi daga Rigasa 14:00 ya sauka a Idu 16:07.”
Sanarwar na zuwa ne kwana hudu bayan gwamnati ta dage ranar dawowar jiragen, a jajibirin fara zirga-ziargarsu da aka tsara a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba.
Da yake magana kan dawowar jiragen, Fidet ba wa fasinjoji tabbacin samun cikakken tsaro, ya kuma shawarce su da su sabunta manhajarsu ta sayen tikiti daga ranar Asabar, 3 ga watan Disamba da muke ciki.
Idan ba a manta ba, a ranar Lahadi, yayin gwajin jiragen, Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ba da umarnin hana duk wanda ba shi da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) hawa jiragen kasan.
Ministan ya kara da cewa matakan tsaro da Gwamnatin Tarayya ta sanya gabanin fara zirga-zirgar jiragen sun kai kashi 90 cikin 100 a lokacin.
Tun ranar 28 ga watan Maris, 2022 aka dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna, bayan ’yan bindiga sun kai masa hari sun kashe fasinjoji 10, suka sace wasu 60, sai bayan watanni suka sako su.