Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna zai koma da aiki ranar Asabar

Za a ci gaba da zirga-zirgar jirgin ranar Asabar 23 ga Oktoba, 2021.

Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna zai koma da aiki ranar Asabar

Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta sanar cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ranar Asabar.

Hukumar ta sanar da hakan ne ranar Juma’a bayan harin nakiya da ya lalata layin dogon a ranakun Laraba da Alhamis.

Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Juma’a da dare ta ce an kammala aikin gyaran layin dogon kuma komai ya daidaita.

“NRC na sanar da al’umma musamman fasinjojinmu cewa zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna (AKTS) zai ci gaba gobe Asabar, 23 ga watan Oktoba, 2021,” inji sanarwar da Mataimakin Daraktan Yada Labaran Hukumar ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa jiragen farko da za su tashi ranar Asabar din su ne kamar haka:

“Daga IDU, Abuja (AK3) zai tashi 09:50 na safe. Daga RIGASA, Kaduna kuma (KA4) da karfe 10:35 na safe. sannan za a ci gaba da zirga-zirga daga baya. NRC na kara bayar da hakuri saboda tasgaron da aka samu.”