Jirgin kasar Habasha ya fara zirga-zirga daga Addis Ababa zuwa Kaduna
Kamfanin Jirgin Sama na kasar Habasha watau Ethiopian Airlines ya fara zirga-zirga daga babban Birnin kasar Addis Ababa zuwa filin jirgin saman Kaduna. Ranar Talatar nan ne da ta gabata jirgin ya bar Birnin Addis Ababa, inda ya sauka a filin jirgin saman Kaduna da misalin karfe 11:30 na safe. Gwamnar jahar Kaduna Nasir Ahmad […]

Kamfanin Jirgin Sama na kasar Habasha watau Ethiopian Airlines ya fara zirga-zirga daga babban Birnin kasar Addis Ababa zuwa filin jirgin saman Kaduna.
Ranar Talatar nan ne da ta gabata jirgin ya bar Birnin Addis Ababa, inda ya sauka a filin jirgin saman Kaduna da misalin karfe 11:30 na safe.
Gwamnar jahar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai tare da wasu jami’an gwamnatinsa ne suka tarbi jirgin a Kaduna.
Da yake jawabi El-Rufai ya ce fara zirga-zirgar jirgin a jihar zai taimaka matuka wajen inganta tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya kuma tabbatarwa da hukumomin kamfanonin Jiragen saman Habasha cewa gwamnatin sa za ta taimaka matuka wajen ganin cewa hada-hadar suifurin ta dore.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi murnar wannan sauka da jirgin Habasha a karon farko ya yi a Kaduna, domin muna da tabbacin hakan zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin Jihar Kaduna. Wannan wani mataki ne da zai taimaka wa jihar nan wajen inganta tattalin arzikinta da kuma sauran hulda da wasu kasashe, musamman zai taimaka wa ’yan kasuwa masu zuwa kasashen waje domin yin harkokinsu,” inji shi.
Gwamna El-Rufai ya kara da cewa gwamnatin jiha da ta tarayya sun zuba jari wajen gyaran filin jirgin saman Kaduna a lokacin da aka rufe na Abuja, don haka suka ga ya dace a cigaba da amfani da shi domin cigaban kasar nan.
“Wannan zirga-zirgar jirgin Habasha zuwa Kaduna ya fi sauki ga mutane mazauna yankin Arewa maso Gabas zuwa Abuja. Za kuma mu cigaba da tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar jiragen sama, domin janyo wasu kamfanonin jiragen sama zuwa Kaduna,” inji shi.
Da yake jawabi a wajen, Jakadan kasar Habasha a Najeriya Samia Zakariya Gutu ya ce matafiya daga Kaduna suna da damar ziyartar kasashe sama da dari a duniya.
Ya ce kanfanin jirgin a shirye yake ya biya wa matafiya bukatarsu cikin sauki.