Jirgin ‘leken asiri’ ya fado a Jihar Kaduna
A ranar Alhamis da ta gabata ne wani jirgin sama da ake zaton na leken asiri ne ya fado a kauyen Maidaro a yankin Kidandam ta karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna, inda ya sa dar-dar a zukatan mazauna kauyen.Hakimin Kidandam kuma Kaigaman Zazzau, Alhaji Umar ya tabbatar wa wakilinmu cewa ya ga jirgin […]

A ranar Alhamis da ta gabata ne wani jirgin sama da ake zaton na leken asiri ne ya fado a kauyen Maidaro a yankin Kidandam ta karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna, inda ya sa dar-dar a zukatan mazauna kauyen.
Hakimin Kidandam kuma Kaigaman Zazzau, Alhaji Umar ya tabbatar wa wakilinmu cewa ya ga jirgin kafin a dauke shi zuwa hedikwatar ’yan sandan Jihar Kaduna.
Ya ce jirgin dan karami ne da za a iya dauka da hannu daya. “Jama’a sun firgita suna tunanin cewa daya daga cikin jiragen da ake amfani da su ne wajen kai makamai ga ’yan ta’adda da suke boye a daji,” inji shi.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna ASP Aminu Lawal ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da bincike don sanin matsayin wannan jigi.
Ya ce ba wani abin tashin hankali ba ne, amma kamata ya yi mutum ya halarci wurin da abin ya fado don tattaunawa da wadanda ya fado a gabansu.
Wani na kusa da fadar gwamnatin Jihar Kaduna da bai so a ambaci sunansa ba ya ce jirgin na rundunar sojar sama ta Kaduna ne kuma an kera shi ne a bara domin tattaro bayanai a dazukan da mabarnata ke boyewa kuma an sa wa jigin suna gulma.
Wani kwararre kan harkokin jiragen sama ya ce jiragen leken asiri mafi yawancinsu ’yan kanana ne da za a iya dauka da hannu daya, kuma ana sarrafa su ne daga kasa. Saboda haka, na iya yiwuwa jirgin da ya fado na leken asiri ne.