Jirgin Max Air da ya makale da alhazai a Nijar ya samu izinin tashi

Jirgin ya tafi birnin Jidda na kasar Saudiyya domin kwaso ragowar alhazan Najeriya zuwa gida

Jirgin Max Air da ya makale da alhazai a Nijar ya samu izinin tashi

Jirgin kamfanin MaxAir da ke jigilar alhazan Najeriya wanda ya makale a Jamhuriyar Nijar sakamkon juyin mulki ya samu izinin tashi.

Hukumar gudanarwar MaxAir ta sanar cewa tuni jirgin samfurin Boeing 747-400 ya bar kasar zuwa birnin Jidda na kasar Saudiyya domin kwaso ragowar alhazan Najeriya zuwa gida.

Kamfanin ya fitar kafin wayewar garin Juma’a, awanni bayan makalewar jirgin a kasar Nijar, yana godiya ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya da suka sanya baki aka saki jirgin.

A ranar Alhamis MaxAir ya tabbatar da cewa jirinsa mai lamba 5N-ADM, an hana shi tashi ne bayan ya sauke rukunin karshe na alhazan Nijar, a ranar da sojojin kasar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.

MaxAir na daga cikin kamfanonin jiragen sama na cikin gida a Najeriya da Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta ba wa aikin jigilar alhazai a bana.

Kamfanin wanda mallakin attajiri dan asalin jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal ne, ya jima yana wannan aiki.