Jirgin ruwa ya fashe,ya kashe mutum guda

    Fasinja daya ya mutu, wadansu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a lokacin da ake yi wa wani jirgin ruwan daukar fasinja karin mai a gabar tekun Legas.Lamarin, wanda  ya auku a karshen makon da ya gabata, ya sanya mutane cikin fargaba, inda suka gigice suka rika gudu […]

Jirgin ruwa ya fashe,ya kashe mutum guda
Jirgin ruwa ya fashe,ya kashe mutum guda

 

 

Fasinja daya ya mutu, wadansu da dama sun samu munanan raunuka sakamakon gobarar da ta tashi a lokacin da ake yi wa wani jirgin ruwan daukar fasinja karin mai a gabar tekun Legas.
Lamarin, wanda  ya auku a karshen makon da ya gabata, ya sanya mutane cikin fargaba, inda suka gigice suka rika gudu saboda sun yi tsammanin bom ne ya tashi a gabar tekun saboda karar da suka ji, ta fashewar jirgin.
Binciken Aminiya ya gano cewa da farko gawar daya daga cikin fasinjojin jirgin mai suna Emmanuel Omu, dan kimanin shekaru 28, ta bace, sai daga bisani rundunar hadin gwiwa ta ma’aikatan hukumar agajin gaggawa ta NEMA da ’yan sandan da ke aiki a ofishin ’yan sanda na gabar tekun suka gano ta a cikin teku.
Jirgin, wanda ake ce na kamfanin hada-hadar mai ne mai suna Akuiten Oil and Gas ya yi ta cin wuta na tsawon sa’o’i, kafin a shawo kan gobarar.
Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta NEMA, Malam Ibrahim Farinloye ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce, “Mun samu labarin bindigar da jirgin ruwa ya yi, a ranar Juma’a, wanda ya yi wa fasinjoji rauni, wadanda aka kai musu dauki zuwa asibitoci da daban-daban.”
Ya ci gaba da cewa, “Jirgin ya tashi daga tashar ruwan da ake kira ‘b Craft Jetty’ da ke rukunin yankin unguwar Lekki ta daya, a lokacin da yake shan man gas a tashar da ake kira ‘Capital Oil Jetty’ da ke yankin bictoria Island, sai injinsa ya yi bindiga.”