Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato
Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwan.
Wani jirgin ruwa ɗauke da mutum sama da 30 da kuma babura takwas, ya nutse a garin Kojiyo da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru Goronyo, ya ce jirgin ya yi hatsari ne a kogin garin bayan ya ɗauki mutane da kaya da suka fi ƙarfinsa.
- Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari/Tsanyawa
- Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025)
Ya ce: “Mutane 30 da jirgin ya ɗauka ba a ga ko ɗaya daga cikinsu ba tukuna.
“Sai dai an fitar da babur guda ɗaya daga cikin takwas da suka nutse, amma kayan da mutane duk sun ɓace.”
Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomi.