Jirgin sama ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi ya ɓace

Hukumomi a ƙasar ba su sake jin ɗuriyar jirgin ba tun bayan tashinsa.

Jirgin sama ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi ya ɓace

Wani Jirgin Saman Soji ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Mawali, Saulos Chilima tare da wasu mutum tara ya yi ɓatan-dabo.

Wannan na cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Litinin.

Jirgin da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar mai sheka de a 51, ya bar babban birnin ƙasar, Lilongwe a ranar Litinin amma ba a sake jin ɗuriyarsa ba.

“Na’ura ba ta sake jin motsin jirgin sojojin ƙasar ta Malawi ba, bayan ya tashi daga Lilongwe, babban birnin ƙasar a safiyar yau Litinin.”

Shugaban ƙasar Lazarus Chakwera, ya bayar da izinin fara aikin bincike da na ceto bayan ma’aikatan jiragen sama a ƙasar sun ce sun kasa yin magana da matuƙan jirgin.

Asali dai jirgin na kan hanyarsa ne zuwa filin jirgi na Mzuzu da ke Arewacin ƙasar, inda ake sa ran zai isa da misalin ƙarfe 11 na safe.

Tuni shugaba Lazarus Chakwera, ya soke wata tafiya da ya shirya yi zuwa Bahamas.