Jirgin sama dauke da mutane 378 ya kone a Japan
Wani jirgin sama dauke da mutane 379 ya kama da wuta a Filin Jirgi na Haneda da ke kasar Japan.
Wani jirgin sama dauke da mutane 379 ya kone kurmus bayan da ya kama da wuta a sakamkon hatsari a Filin Jirgi na Haneda da ke kasar Japan.
Ministan sufuri na kasar, Tetsuo Saito, ya sanar da rasuwar mutane 5 a sakamakon a hatsarin, wanda wasu jirage biyu suka yi karo a ranar Talata.
Ma’aikatar sufurin kasar Japan ta ce, mutane biyar da ke cikin wani karamin jirgin gadin gabar teku suka mutu, bayan da ya yi karo da wani jirgi kirar Airbus na kamfanin Japan Airlines a filin jirgin.
Ministan ya bayyana cewa an yi nasarar fitar da fasinjoji 367 da ma’aikata 12 da ke cikin jirign Japan Airlines din da ransu, duk da cewa jirgin da suke ciki ya kama da wuta.
Amma biyar daga cikin ma’aikata shida da ke karamin jirign kuma sun rasu, a yayin da suke hanyarsu zuwa tsakiyar kasar domin aikin agaji saboda girgizar kasa da aka samu ranar Litinin.
Ministan sufurin ya bayyana cewa matukin karamin jirgin da ya tsira, ya samu rauni, kuma kawo yanzu ba a gano musabbabin hatsarin jirgin ba.