Jirgin sama ya dira a kan titin mota

Wani jirgin saman fasinja a Iran ya kaucewa hanyarsa ta sauka inda ya dira a kan titin mota. Biyu daga cikin fasinjoji 136 da ke cikin jirgin sun samu rauni a kafa a hadarin wanda ya faru a birnin Mahshahr, kamar yadda likitoci suka bayyana. Jirgin na Caspian Airlines sanfurin McDonnell Douglas MD-83 ya taso […]

Jirgin sama ya dira a kan titin mota

Wani jirgin saman fasinja a Iran ya kaucewa hanyarsa ta sauka inda ya dira a kan titin mota.

Biyu daga cikin fasinjoji 136 da ke cikin jirgin sun samu rauni a kafa a hadarin wanda ya faru a birnin Mahshahr, kamar yadda likitoci suka bayyana.

Jirgin na Caspian Airlines sanfurin McDonnell Douglas MD-83 ya taso ne daga birnin Tehran.

Gidan talbijin na kasar ya ambato jami’an yankin na cewa matukin jirgin ne “ya yi jinkiri wurin sauka abin da ya ya kaucewa titinsa”.

Mohammad Reza Rezaei ya kara da cewa wannan ne “ya sa jirgin ya zarce hanya sannan ya dira a wani wuri” da ke kusa da filin saukar jiragen.

NAJERIYA A YAU: Haƙiƙanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Edo

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

Tags