Jirgin saman da ake koyo ya yi hadari a Ilori
Wani jirgin saman da ake horar da matuka jiragen sama mallakin kwalejin al’amuran sufurin jirgin sama na duniya ya yi hadari a filin jirgin saman Ilorin babban birnin jihar Kwara a jiya Laraba. Jirgin saman mai lamba 5N-BNH da direbobi biyu ya yi hadari ya fado a daidai karfe 11:05 na safe, an samu rahoton […]
Wani jirgin saman da ake horar da matuka jiragen sama mallakin kwalejin al’amuran sufurin jirgin sama na duniya ya yi hadari a filin jirgin saman Ilorin babban birnin jihar Kwara a jiya Laraba.
Jirgin saman mai lamba 5N-BNH da direbobi biyu ya yi hadari ya fado a daidai karfe 11:05 na safe, an samu rahoton faduwar jirgin a yau Alhamis.
Wannan hadarin jirgin ya janyo jinkiri a tashar jiragen saman Ilorin, wanda hakan ya haddasa jinkirin awa 3 na matafiya da ke shirin tafiya daga tashar jiragen saman jihar.