Jirgin soji ya tarwatsa rumbum makaman Boko Haram
Jiragen sojin saman Najeriya sun tarwatsa wani babban rumbun makaman Boko Haram a Jihar Borno
Dakarun Sojin Sama na Operation Hadin Kai (OPHK) sun tarwatsa wani babban rumbun ajiye makamai na ’yan ta’addar Boko Haram.
Wata majiyar tsaro ta ce, “an kai hain ne kai-tsaye kan wani wurin da ake zargin ma’ajiyar makaman Boko Haram ne.
“Harin ya kona rumbun makaman shi dungurungum dinsa, tare da kashe da yawa daga cikin ’yan kungiyar, yayin da wasu suka tsira da munanan raunuka.”
Rahotanni sun nuna rumbun makaman yana yankin Amchile da ke yankin Gezuwa da ke kusa da Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.
- Osimhen da Asisat Oshiola sun zama gwarazan ’yan wasan Afirka na 2023
- Yadda Ma’aikaciyar Gwamantin Kano Ta Rasu Saboda Rashin Samun Albashi
Sojojin saman Najeriya sun kai harin ne a ranar 9 ga watan Disamba, bayan samun rahotanni da ke nuna akwai gungun wasu ’yan Boko Haram a wurin.
Majiyoyin tsaro sun shaidawa Zagazola Makama, kwararre kan Yaki da Ta’addanci a yankin tafkin Chadi cewar jiragen sojin sun kai hari a yankin sun kashe dimbin ’yan ta’addan baya ga makaman da aka lalata da yawan gaske.