Jirgin sojin Najeriya ya fado a Kaduna

Jirgin sojin ya fado ne a yayin da yake tsaka da aikin sintiri domin samar da tsaro

Jirgin sojin Najeriya ya fado a Kaduna

Jirgin da ya yi hatsari

Wani jirgin sama na sojin Najeriya ya yi hatsari a kauyen Tami da ke yankin Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin ya ce jirgin sojin ya yi hatsari ne da misalin karfe 5 na asubar Litinin din nan.

Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa matukin ya fito daga cikin tarkacen jirgin da ya fado.

Bayan nan sojoji suka yi gaggawar zuwa suka yi wa yankin kawanya tare da fara bincike.

Sojojin sun kuma hana mutane isa wurin da tarkacen jirgin yake.

An ce jirgin yana tsaka da aikin sintiri a yankin ne ya samu matsala, lamarin da ya haddasa fadowarsa.

Kawo yanzu Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ba ta fitar da sanarwar game da lamarin ba.

Kakakin rundunar a Jihar Kaduna, Alaere Eyinimiere Obidake, ya ki daga kiran da muka yi masa domin neman bahasi.

Wakiliyarmu ta yi ta kiran shi, amma yana yanke kiran.