Jerin hatsarin jiragen sojin Najeriya a 2023

Sau hudu jiragen sojin Najeriya suka yi hadari a 2023

Jerin hatsarin jiragen sojin Najeriya a 2023

Tsohon hoto

Wani jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ya yi hatsari a yayin da yake aikin yaki da masu satar danye mai a Jihar Ribas.

Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya tabbatar da hatsarin jirgin da cewa fasinjojin sun tsira da raunuka.

Ya bayyana cewa Babban Hafsan Rundunar, Air Marshal Hasan Abubakar, ya ziyarci wurin domin “duba lafiyar sojojin da kuma gane wa kansa abin da ya faru.”

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin hatsarin helikwaftar kirar MI-35P ba.

Hatsarin jiragen soji a 2023

Jirgin da ya fado a safiyar Juma’a a garin Fatakwal, shi ne na hudu a jiragen sojin Najeriya da suka yi hadari a shekaran nan ta 2023.

Na hudunsu kuma na koyon tukin jirgi ne wato Flight Trainer.

  1. 6 ga Fabrairu: jirign soji kirar Cessna Citation CJ3 da ke aikin sintiri a teku ya ci kasa da Jihar Legas, sakamakon rashin tayoyyi.
  2. 14 ga Yuli: Jirgin soji FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi, Jihar Binuwai, amma matukansa da ake ba wa horo sun tsira kamar na farkon.
  3. 14 ga Agusta: Helikwaftan soji MI-171 da ya je kwaso gawarwaki da dakarun da suka samu rauni ya yi hatsari a kauyen Chukuba na Jihar Neja.
  4. 1 ga Disamba: Helikwaftan soji dake yaki da barayin mai ya yi hatsari da misalin karfe 7.45 na safiya a Fatakwal, Jihar Ribas.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos