Jirgin sojin Rasha ya fado a kusa da Ukraine

Hatsarin ya afku ne a wani daji mai nisan kilomita 150 daga kan iyakar Rahsha da kasar Ukraine

Jirgin sojin Rasha ya fado a kusa da Ukraine

Taswirar kasar Rasha (AFP)

Wani jirgin sojin kasar Rasha samfurin Mi-28 ya fado a wani yanki da babu kowa a Kudu maso yammacin kasar.

Hatsarin jirgin mai saukar ungulu ya yi ajalin ma’aikatan jirgin, kamar yadda wasu kamfanonin dillancin labaran kasar Rasha suka sanar a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na TASS ya ambato wata majiya a ma’aikatar tsaro ta ce “helkiwafta kirar Mi-28 ya fado a yankin Kaluga… ma’aikatan jirgin sun mutu.”

“Bayanan farko sun nuna wata matsalar fasaha ce ta haddasa hatsarin jirign,” in ji kamfanin dillancin labarai na Interfax, yana ambato wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar.

Hatsarin jirgin sojin ya faru ne  ne a wani daji mai tazarar kilomita 150 daga kan iyakar kasar Rasha da Ukraine, kamar yadda wani jami’in yankin ya shaida wa TASS.

Hadarin ya afku ne a wani daji mai nisan kilomita 150 daga kan iyakar kasar ta Ukraine.

AFP

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe