Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja

Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja

Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja.

Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa.

Majiyoyi sun ce jirgin ya samu matsala ne,  lamarin da ya sa matuƙan jirgin suka ɗauki matakin gaggawa.

Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Ƙarin bayani na tafe…