Jirgin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Neja

Tsautsayi ya rutsa da jirgin wanda ya taso daga Neja zuwa Kaduna.

Jirgin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Neja

Jirgin Sojin Saman Najeriya

Wani jirgin sama mallakar rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ya yi hatsari a Jihar Neja.

Jirgin wanda tsautsayin ya rutsa da shi a wannan Litinin din na kan hanyar zuwa Kadune ne daga ta jihar ta Neja.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar sojin saman, Air Commodore Edward Gabkwetnin, ya ce jirgin mai saukar angulu samfurin MI-171, ya fadi ne da misalin karfe 1.00 na rana a Kauyen Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro a Neja.

A yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da fasinjojin jirgin, Mista Gabkwetnin ya ce tuni bincike ya kankama domin gano musabbabin faruwar lamarin.