Jirgin yaki ya kashe masu makoki 37 a Nijar
Wani jirgin yaki ya kashe wasu mutane 37 da ke zaman makoki a wani kauye da ke yankin Abadam a jamhuriyar Nijar a ranar Talata. Mataimakin magajin garin Abadam, Ibrahim Ari wanda ya tabbatar faruwar al’amarin ya bayyana mutane fiye da 20 kuma sun jikkata a lokacin da abin ya faru.Ibrahim Ari ya ce jirgin […]
Wani jirgin yaki ya kashe wasu mutane 37 da ke zaman makoki a wani kauye da ke yankin Abadam a jamhuriyar Nijar a ranar Talata.
Mataimakin magajin garin Abadam, Ibrahim Ari wanda ya tabbatar faruwar al’amarin ya bayyana mutane fiye da 20 kuma sun jikkata a lokacin da abin ya faru.
Ibrahim Ari ya ce jirgin yakin ya saki bama-bamai uku ne, inda daya ya fada tsakiyar masu zaman makokin, yayin da biyu kuma suka fashe a wajen gari.
Dakarun kawance da suka hada da na Najeriya da Nijar da kuma Chadi na kai farmaki kan maboyar ’yan kungiyar Boko Haram ta sama da ta kasa. Abin da ya sa wadansu ke ganin mai yiwuwa jirgin ya yi tsammanin masu zaman makoki da cewa ’yan Boko Haram ne.
Sai dai kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Chris Olukolade ya ce bashi da labarin wani jirgi na kasar ya harba bam a kan masu zaman makoki.