Jirkita sunan dan takara zai jawo matsala ga sabon shugaban PDP

daya daga cikin wadanda su ka nemi kujerar shugabancin PDP a yayin zabenta na cike gurabun ’yan majalisar zartarwa na kasa a ranar 9 ga watan nan, Farfesa Taoheed Adedoja ya maka jam’iyyar a kotu inda ya ke neman kotun da ta soke zaben tare da sake yin wani kan zargin sauya masa suna da […]

Jirkita sunan dan takara zai jawo matsala ga sabon shugaban PDP

daya daga cikin wadanda su ka nemi kujerar shugabancin PDP a yayin zabenta na cike gurabun ’yan majalisar zartarwa na kasa a ranar 9 ga watan nan, Farfesa Taoheed Adedoja ya maka jam’iyyar a kotu inda ya ke neman kotun da ta soke zaben tare da sake yin wani kan zargin sauya masa suna da aka yi, inda ya danganta hakan da rashin nasarar da ya yi. 

Farfesa Adedoja wanda tsohon ministan wasanni da matasa ne, ya ce sunan da aka sa a jikin katin zaben shi ne Taoheed Oladoja a maimakon Taoheed Adedoja wanda kuma shi ne sunan da ’yan uwa da sauran magoya bayansa su ka san shi da shi, in ji shi.

A bayanin karar wanda ya ce lauyansa Mista Rickey Tarfa ya shigar, tsohon dan takarar ya nemi kotun da ta hada har da hukumar zabe ta kasa da kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren zaben wanda shi ne gwanan jihar Delta, Mista Ifeanyi Okowa a matsayin wadanda za su gurfana a gaban kotun. Farfesa Adedoja wanda ya bayyana matsayar tasa a yayin wata zantawa da ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana bukatun nasa kamar haka:

Ayyana zaben Mista Uche Secondus a matsayin haramtacce, a soke zaben, aiwatar da wani sabon zabe cikin kwana 30 bayan soke shi, hana hukumar zabe daukar Mista Secondus a matsayin jagoran jam’iyyar, da dai sauransu. “Na shiga takarar ce cike da burin gyara jam’iyya, inda na zagaya sassan kasar nan daban-daban don neman amincewar masu zabe, tare da biyan duk wani kudi da jam’iyya ta daura mini, sannan aka gayyace ni wajen tantance ’yan takara inda a ka ayyana ni a matsayin wanda ya cancanta ya nemi kujerar.

“A lokacin da aka zo yin zaben wasu daga cikin ’yan takarar sun janye sai dai ni ban janye ba, amma a maimakon a yi mana zaben adalci sai aka jirkita sunana da gangan zuwa sunan da masoyana ba su sanni da shi ba.  “A dukkan zabukan da aka sani ana kafa kwamitin sauraron korafi bayan zabe, amma ba a samu irin haka ba a wannan sai dai kwamitin sasantawa wanda kuma har zuwa yau din nan ba su zauna da ni ba in banda sauran ’yan takara daga bangaren Kudu maso Yamma. “A saboda haka na dauki matakin neman hakkina a gaban kotu kuma ina da yakinin cewa zan samu nasara, inji Adedoja.